ترجمة سورة التكوير

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة التكوير باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Idan rãna aka shafe haskenta
Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
____________________
 * Rãƙuma mãsu ciki ɗan wata gõma.
Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu.
____________________
 * Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta.
Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta.
____________________
 * A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure.
"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba.
____________________
* Masu tafiya suna kõmawa bãya.
Mãsu gudu suna ɓũya.
Da dare idan ya bãyar da bãya.
Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
Kuma lalle ne, yã gan shi(5) a cikin sararin sama mabayyani.
____________________
  (5) Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya.
Kuma shi, ga gaibi(6) bã mai rowa ba ne.
____________________
   (6) Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.
Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
Shin, a inã zã ku tafi?
Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.
Icon