ترجمة معاني سورة المسد باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation . ﰡ ﮈﮉﮊﮋﮌ ﰀ Al-MasadHannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka. ﮎﮏﮐﮑﮒﮓ ﰁ Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra. ﮕﮖﮗﮘ ﰂ Zã ya shiga wuta mai hũruwa. ﮚﮛﮜ ﰃ Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta). ﮞﮟﮠﮡﮢ ﰄ A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma).