ترجمة سورة المسد

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة المسد باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka.
Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra.
Zã ya shiga wuta mai hũruwa.
Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta).*
____________________
  * Anã fassara shi da mai tsegumi, wãtau annamĩmanci; da Lãrabci anã ce wã mai annamĩmanci "mai ɗaukar itacen wuta.".
A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma).
Icon