ﰡ
Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce.
Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu).
Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa.
Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci."
"Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!"
Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!"
"Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya."
"Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba.
Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta?
Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu).
Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu.
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa).
Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, *waɗancan ne ƙungiyõyin.
____________________
* Mutãnen ƙunci, sũ ne mutãnen Annabi Shu'aibu. A cikin Sham suke.
Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba.
Kuma waɗannan *bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani.
____________________
* Watau mutãnen Annabi Muhammadu: Ƙuraishãwa da waninsu har ya zuwa Tashin Ƙiyãma.
Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike."*
____________________
* Wannan ita ce maganar dukan kãfirai na kõwane zãmani mãsu nħman rabon dũniya kawai, ba su yarda da Tãshin Ƙiyãma ba, balle sãmun sakamako a cikinsa.
Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwanMu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne.
Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã.
Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi.
Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima* da rarrabẽwar magana.
____________________
* Hikima, ita ce Annabci, rarrabe magana, shĩ ne sanin hanyar yin sharĩ'a da rarrabe mai ƙãra daga wanda aka yi ƙãra, da neman shaidu daga mai ƙãra da neman rantsuwa ga mai musu.
Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci?
A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya."
"Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana."
(Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce* ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
____________________
* Dãwũda ya yi hukunci da zãlunci ga wanda ya yi ƙãra, sabõda abin da ya rufe shi na ƙin zãluntar mai rauni wanda Allah Ya hana. Nauyin wani laifi ya rufe shi daga tunãwa da wani laifi, watau yin hukunci tun binciken shari'a bai cika ba, sabõda iya maganar wani abõkin ƙãra. Wannan shĩ ne fitinar da ta same shi kawai kuma a kanta ya yi nadãma, kuma a kanta ne Allah Ya yi masa gargaɗin kada ya bi son rai mai sanya Fushi kõ yarda ga abin da bai cancanci haka ba. Yarda da wata ƙissar mãtar Uriya wadda Yahũdãwa ke sanyãwa, a nan, kãfirci ne ga Musulmi, dõmin ta kõre ismar Annabãwa, kuma ba ta dãce da lafazin Alƙur'ãni ba.
Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurinMu, da kyaun makõma.
Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi
Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã.
Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata?
(Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.
Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah.
A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, *a lõkacin maraice.
____________________
* Shĩ ne dõki mai tsayuwa a kan ƙafãfu uku. Wannan yanã nũna asalinsa mai kyau ne.
Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki!"
"Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu* da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.
____________________
* Sulaimãna ya yanka dawãkin,dõmin kallonsu yã hana shi salla, wadda take farlu ainin ce a gare shi, amma tattalin kãyan yãƙi farlu kifãya ce. Anã gabãtar da farlu ainin a kan farlu kifãya. Wannan kuma ya nũna cewa anã cin dõki idan wani dalĩli bai hana ba. Dũbi Sũra ta 16, ãyã ta 8.
Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini* Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.
____________________
* Wata rãna Sulaiman ya yi tunãnin ya sãdu da mãtansa ɗari uku, dõmin su yi cikunna su haifi diya mãsu taimakonsa jihãdi fi sabilillahi, amma ya manta, bai ce in Allah Yã so ba. Sai ya sãdu da su, ba su yi cikin ba, sai guda ɗaya daga cikinsu, kuma ta haife shi bãbu rai. Ma'anar kissar, ita ce ko aikin Allah, sai mutum ya mayar da yinsa ga mashĩ'ar Allah, sa'an nan zai ci nasara a kansa.
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna.* Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
____________________
* Yã yi wannan addu'a dõmin kada wani ya yi alfahari da sarauta a bãyansa, ya halaka kuma ya halakar da wani. Sarauta ita ce asalin girman kai da alfahari. Bã ka ganin wanda ya shiga wajan sarki, dõmin ya gaishe shi, idan ya fito daga gare shi, sai ya ɗõra yin tãƙama dõmin abin da zuciyarsa ta ɗebo daga girman kan sarkin da alfaharinsa?.
Sabõda haka Muka hõre masa iska(5) tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa.
____________________
(5) An hore masa iska matsayin dawãkin da ya yanke dõmin Allah. An hõre masa aljannu dõmin niyyarsa ta sãmun diya mãsu jihãdi dõmin Allah.
Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.)
Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa.
Wannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike.
Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma.
Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba(6) a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."
____________________
(6) Wannan ƙissa tanã nũna haƙuri ga riƙon iyãli, mulkin ƙasã da mulkin gida duka daidai suke, sai yadda Allah Ya yi umurni a yĩ su. Haka mallakar rai idan mutum bai bi umurnin Allah ba a cikinsu, sai su buwãye shi tsarewa, kamar yadda mulkin ƙasa ke buwãya a riƙe shi tãre da kãfirci da zãlunci.
Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã.
Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali.
Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne.
Kuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurninMu) da basĩra.
Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira).
Kuma lalle sũ a wurinMu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta.
Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu.
Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma.
Gidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su.
Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã.
Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna.
Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi.
Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwarMu ce, bã ta ƙãrẽwa.
Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma.
Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita.
Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini.
Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i.
Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne.
Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar).
Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã."
Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?"
"Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?"
Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã.
Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa."
"Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara."
Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma".
"Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!"
"Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma."
"Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa."
A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã.
"Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga RuhĩNa a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi."
Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya.
Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
(Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne?"
Ya ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã."
Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne."
"Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako."
Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su."
Ya ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri,
"Zuwa ga yinin lõkaci sananne."
Ya ce, "To, inã rantsuwa da buwãyarKa, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya.
"Fãce bãyinKa tsarkakakku daga gare su."
(Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa."
"Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya"
Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa."
"Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta."
"Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa* a bayan ɗan lõkaci."
____________________
* Bauta wa gumãka da hidimar shehunai da suka mutu waɗanda suka shirya wani sãbon abu da bãbu ga sunnar Annabi duka ɗaya suke, dõmin kõwanensu kiran wanin Allah ne sabõda neman ãgaji.