ترجمة معاني سورة التوبة باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation

Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation


Sa'an nan idan sun tũba kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.

Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãninsu sunã hanuwa.

Ku yãƙe su, Allah Ya yi musu azabã da hannãyenku, kuma Ya kunyatar da su, kuma Ya taimake ku, kuma Ya warkar da ƙirãzan mutãne mũminai.

Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi, a cikin hanyar Allah, da dũkiyõyinsu, da rãyukansu, sũ ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah, kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.

Ubangijinsu Yanã yi musu bishãra da wata rahama daga gare shi, da yarda, da gidãjen Aljanna. sunã da, a cikinsu, ni'ima zaunanniya.

Ka ce: "Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da mãtanku da danginku da dũkiyõyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsõron tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya sõyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihãdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah Ya zo da umurninSa! Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai."

A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska."

Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.

Abin sani kawai, "Jinkirtãwa" ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.

Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya musanya wasu mutãne, wasunku (a maimakonku). Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.

Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: "Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yanã tãre da mu." Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.

Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.

Dã yã kasance wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa. Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah, "Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.'

Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin kai kãwo.

Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,

Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro.

Kuma lalle ne, idan ka tambaye, su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"

Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare su, kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa.

Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, "Lalle ne idan ya kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã kasancẽwa, daga sãlihai."

To, a lõkacin da Ya bã su daga falalarSa, sai suka yi rõwa da shi, kuma suka jũya bãya sunã mãsu bijirẽwa,

Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatansu har zuwa ga Rãnar da suke haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda abin da suka kasance sunã yi na ƙarya.
آية رقم 82

Sabõda haka su yi dãriya kaɗan, kuma su yi kũkada yawa a kan sãkamako ga abin da suka kasance sunã tsirfatãwa.

To, idan Allah Ya mayar da kai zuwa ga wata ƙungiyã daga gare su sa'an nan suka nẽme ka izni dõmin su fita, to, ka ce: "Bã zã ku fita tãre da nĩ ba har abada, kuma bã zã ku yi yãƙi tãre da nĩ ba a kan wani maƙiyi. Lalle ne kũ, kun yarda da zama a farkon lõkaci, sai ku zauna tãre da mãtã mãsu zaman gida."

Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama (a cikin gidãje). Kuma aka rufe a kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta.

Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da ManzonSa da Muminai kuma zã a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Kuma waɗanda suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa, su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.

Lalle ne, Allah Ya saya daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ su. (Allah Yã yi) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma.

Mãsu tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai.

Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi (Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri.

Bã ya kasancẽwa ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.

Kuma bã ya kasancẽwã ga muminai su fita zuwa yãƙi gabã ɗaya. Sabõda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita (zuwa nẽman ilimi ba) dõmin su nẽmi ilimi ga fahimtar addĩni kuma dõmin su yi gargaɗi ga mutãnensu idan sun kõma zuwa gare su, tsammãninsu, sunã yin sauna?

Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai.

Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
تقدم القراءة