ﰡ
____________________
* Laifin Annabi wanda Allah Ya gãfarta, shĩ ne a lõkacin da ya fãra kiran mutãne zuwa ga bauta wa Allah, Shĩ kaɗai, mãsu bauta wa waɗansu abũbuwa sun ga laifinsa a wannan, sun yi ƙiyayya da shi sabõda haka, har suka yi yãƙi da shi, dõmin tsare ibãdarsu, da al'adunsu, har a lõkacin da Allah Ya bã shi rinjãye bayyananne a kansu, suka gãne amfãnin abin da yake kiran su zuwa gare shi na alheri, suka yãfe laifin da suke zato kuma suka so shi son da bã ya ƙãrewa har Tãshin Ƙiyãma. Wannan ni'imar Allah ce babba ga Annabinsa, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanya madaidaiciya, ita ce sharĩ'ar da Allah Ya bã shi, wadda ke jan jama'arsa a kan alheri har ya zuwa Tãshin ƙiyãma, kuma su tãshi a cikin alheri mafi girma, matuƙar dai sun bĩ ta, sun yi aiki da ita gwargwadon yadda ya nũna musu ita.
____________________
* Asalin mubãya'a daga bai'u ne, watau ciniki, wanda ya yi mubãya'a ga Limãmin Musulmi kamar yã yi ciniki ne yã sayar da ransa, dõmin ya karɓi Aljanna daga Allah a Rãnar Ƙiyãma. Mubãya'a ta farko,ita ce wadda aka yi wa Annabi a Hudaibiyya wani ɗan gari ne kusa da Makka a hanyar Jidda, tafiyar kwana ɗaya. An ce tanã cikin Hurumi, waɗansu sun ce bã ta cikinsa.
____________________
* Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya yi nufin tafiya Makka dõmin ya yi Umra sabõda mafarkin da ya yi cewa yã ga ya shiga Makka shi da Sahabbansa, sunã mãsu yin aski da saisaye na ibãda, sai ya ce wa ƙauyãwan da ke gefen Madina su fita tãre da shi dõmin kada Ƙuraishãwa su fãɗa shi da yãƙi,su tsare shi daga Ɗãkin. Kuma ya yi harama ya kõra hadaya dõmin mutãne su san bã yãƙi yake nufi ba. Sai waɗansu mãsu yawa daga ƙauyãwa suka yi nauyin fita, sukayi zamansu kuma suka ce: "Zai tafi zuwa ga mutãnen da suka yãƙe shi a tsakar gidansa a Madĩna, suka kashe Sahabbansa. Ba zã mu bĩ shi ba dõmin mu halaka kanmu.".
____________________
* A bãyan sulhun Hudaibiyya Allah Ya yi wa Annabi alkawarin zai buɗe masa Haibara ya sãmi ganĩma mai yawa, amma kuma kada ya bari ƙauyãwan da aka nema su fita zuwa Makka, suka ƙi su fita tãre da shi.
____________________
* Abũbakar zai kira su dõmin su yãƙi mutãnen Musailama, ko kuma su yãƙi Rũmu da fãrisa a bãyan rãyuwar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.
____________________
* A bãyan da Annabi ya sauka a Hudaibiyya, ya kirãyi Khuraish bn Umaiya el Khuzã'i ya aike shi Makka ya azã shi a kan rãƙuminsa dõmin ya gaya wa shugabanninsu cewa yãtaho Umra ne, bai zo da yãƙi ba. Sai suka sõke rãƙumin Annabi, kuma suka yi nufin kashe Khuraish amma Ahãbish suka hana su, ya zo ya gaya wa Annabi. Sa'an nan Annabi ya kira Umar bn Khattãb dõmin ya aika shi zuwa Makka, sai ya ce: "Ya Manzon Allah inã tsõron raina ga Ƙuraishãwa, bãbu banĩ Adiyyin bn Ka'ab a Makka balle su kare ni daga gare su, amma inã nũna maka wani mutum wanda ya fĩ ni dangi a cikinta shĩ ne Usman bn Affãn." Sai Annabi ya kira Usman ya aike shi zuwa ga Abi sufyãn da shugabannin Ƙuraish, ya bã su lãbãrin cewa bai zo yãƙi ba. ya taho ne dõmin ziyãra kawai ga wannan Ɗãki dõmin ya girmama alfarmarsa. Ya rubũta masa takarda ya tafi da ita. Kuma ya umurce shi da ya yi bushãra ga Musulmi mãsu rauni, cewa cin nasara yã yi kusa, kuma Allah zai ɗaukaka addininsa. Usman ya fita ya tafi Makka ya iske cewa Ƙuraishãwa sun haɗu a kan hana Annabi shiga Makka. Abban bn sa'ĩd bn Asi ya haɗu da Usman a lõklcin shigarsa Makka, sai ya ɗauke shi a kan rãƙumarsa, ya bã shi maƙwabtaka dõmin kada a kashe shi, har ya kai takardar Annabi. Suka nãce cewa Annabi bã zai shiga ba suka ce wa Usmãn: "Idan yanã son ɗawãfi sai ya yi," Sai ya ce bã zai yi ba sai Manzon Allah ya yi. Musulmi suka ce: "Usmãn ya ji daɗi yã yi ɗawafi," sai Annabi ya ce: "Ban yi zaton Usmãn zai yi ba." Sa'an nan lãbãri ya zo wa Annabi, cewa an kashe Usmãn sabõda haka Annabi ya ce: "Idan sun kashe shi, sai mun yaƙe su." Wannan ya sa aka yi masa mubãya'a a ƙarƙashin itãciyar ɗalh mai kama da farar ƙaya. A bãyan haka Annabi ya aza hannunSa na hagu a kan hannunsa na dãma, ya ce: "Gã hannun Usmãnu." Mãsu mubãya'a dubũ da ɗari uku kõ ɗari huɗu ne, da cewa za su yi yãƙi da Ƙuraishawa, bã zãsu gudu ba, sai dai su mutu. Daga nan shugabancin ya tabbata. Umar bn Khattãb yã sanya an sãre itãciyar nan dõmin mutãne sun fãra salla a ƙarƙashinta. Ba a yi yãƙi ba, sai aka yi sulhu. Annabi ya kõma a shekara mai zuwa yã yi Umra.
____________________
* Cin nasara makusanci, shĩ ne cin Haibara, a bãyan kõmawar Annabi Madĩna a ƙarshen zul Hajji. Sa'an nan ya fita wajen ƙarshen Muharram shekara ta bakwai. Aka samo ganĩma mai yawa. Waɗansu ganĩmõmi na waɗansu ƙasãshen da zã a ci a nan gaba har ƙarshen dũniya. Ganĩmar Haibara ita ce aka gaggauta. ** A lõkacin da Annabi ya fita daga Madĩna zuwa Hudaibiyya Allah Ya kange hannuwan Yahũdãwa daga iyãlan Musulmi na cikin Madĩna, in dã bã dõmin haka ba sai su je su fãɗa su da kashi da kãmu. Sai Allah Ya jefa tsõro a cikin zukãtansu.
____________________
(5) Ganĩma da aka yi musu gaggãwa da ita, ita ce Haibara. Ganĩma wadda ba su da ĩko da ita, ita ce sauran ƙasãshen dũniya inda Musulmi suka ci, suka mallake shi, na ƙasar Rumãwa da farisãwa da Masar da sauransu.
____________________
* Waɗansu Ƙuraishawa ne, sũ tamãnin, suka kewaye Musulmi a Hudaibiyya, da niyyar yaudara, sai aka kãme su, su duka, aka kai su ga Annabi, shi kuma ya yãfe musu, a bãyan ya nũna musu rinjãya. Wannan shĩ ne ya sabbaba yin sulhu.
____________________
* A lõkacin da Ƙuraishi suka ga bã su iya yãƙi da Annabi, suka dõge da ƙabĩlancinsu, ta hanyar sulhu. Suka aika sahlu bn Amru da Huwaitib bn Abdul Uzza da Makraz bn Hafs bn Ahnaf dõmin neman sulhu bisa kada Annabi ya shiga Makka a wannan shekara, amma shekara mai kõmõwa ya je ya shiga Makka kwana uku, su kuma su fita har ya ƙãre Umra ya fita. Annabi ya karɓi sulhun. Aka ce Aliyu bn Abi Talib ya rubũta. Wajen rubũtun kuma aka so a yi tãshin hankali, dõmin ya rũbuta, Manzon Allah ya yi sulhu da Ƙuraishãwa, sai kuma suka ce ba su yarda a rubũta kalmar Manzon Allah ba. Sai Annabi ya sanya hannunsa mai daraja ya sõke kalmar da ake sãɓãni a kanta. Allah Ya saukar da natsuwa ga kõwa. ** Kalmar taƙawa ita ce kalmar shahãda dõmin ɗaukar alkawari da ita yanã lazimtawa mai ita bin umurnin Allah da dãɗi kõ ba daɗi ta haka sai natsuwa ta sãmu. Anã ce mata kalmar taƙawa dõmin da ita ake kãre rai daga bin shaiɗan. Ma'anar taƙawa, ita ce kãriya.
____________________
* Neman falala da sana'ar hannunsu, kõ fatauci, ba su zama nauyi a kan mutãne ba, kõwanensu ya dõgara ga Allah,sa'an nan yanã rãyuwa a kan hãlãliyarsa. ** Kufan sujuda, shĩ ne hasken fuskõkinsu da annurinsu. fuska ita ce madũbin zũciya. Anã gãne zũciyar ƙwarai daga fuskarta. Bã ya halatta ga mutum ya riƙa darkãka gõshinsa ga ƙasã dõmin ya yi kwãdon salla. Wannan alãmar riya ce. Faɗakarwa. Nan ne ƙarshen dõgãyen sũrõri da ake cewa Muɗawwalãtu. An ƙãresu da sũrõri biyu, Ƙitãl dõmin yãƙi, da fat'h dõmin tsãrin gudãnar da siyãsa sabõda tsaron Addĩni. Bãyan haka kuma sai gajerun sũrõri, watau Mufassalãtu.