Fassarar Surar Al-Fatiha a الهوساوية daga Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Verse 1
ﭑﭒﭓﭔ
ﭕ
Al-Fatiha
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
Verse 2
ﭖﭗﭘﭙ
ﭚ
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
Verse 3
ﭛﭜ
ﭝ
Mai rahama, Mai jin ƙai;
Verse 4
ﭞﭟﭠ
ﭡ
Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
Verse 5
ﭢﭣﭤﭥ
ﭦ
Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
Verse 6
ﭧﭨﭩ
ﭪ
Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
Verse 7
Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.
تقدم القراءة