Fassarar Surar At-Tin a الهوساوية daga Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Verse 1
ﭫﭬ
ﭭ
At-Tin
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
Verse 2
ﭮﭯ
ﭰ
Da Dũr Sĩnĩna.
Verse 3
ﭱﭲﭳ
ﭴ
Da wannan gari amintacce.
Verse 4
ﭵﭶﭷﭸﭹﭺ
ﭻ
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
Verse 5
ﭼﭽﭾﭿ
ﮀ
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
Verse 6
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
Verse 7
ﮋﮌﮍﮎ
ﮏ
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
Verse 8
ﮐﮑﮒﮓ
ﮔ
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?
تقدم القراءة