Fassarar Surar Ad-Dhuhah a الهوساوية daga Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Verse 1
ﮉ
ﮊ
Ad-Dhuhah
Inã rantsuwa da hantsi.
Verse 2
ﮋﮌﮍ
ﮎ
Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
Verse 3
ﮏﮐﮑﮒﮓ
ﮔ
Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
Verse 4
ﮕﮖﮗﮘﮙ
ﮚ
Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
Verse 5
ﮛﮜﮝﮞ
ﮟ
Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
Verse 6
ﮠﮡﮢﮣ
ﮤ
Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
Verse 7
ﮥﮦﮧ
ﮨ
Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
Verse 8
ﮩﮪﮫ
ﮬ
Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
Verse 9
ﮭﮮﮯﮰ
ﮱ
Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
Verse 10
ﯓﯔﯕﯖ
ﯗ
Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
Verse 11
ﯘﯙﯚﯛ
ﯜ
Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).
تقدم القراءة