ترجمة معاني سورة الشورى باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation

Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation

آية رقم 1

As-Shurah


Ḥ. M̃.

Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur'ãni) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr.

Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna.

Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa.

Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take."

Kuma Yanã karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yanã ƙãra musu (sakamako) daga falalarSa. Kuma kãfirai sunã da wata azãba mai tsanani.

Kuma abin da ya sãme ku na wata masifa, to, game da abin da hannãyenku suka sana' anta ne kuma (Alah) Yanã Yafẽwar (waɗansu laifuffuka) mãsu yawa.
آية رقم 32

Kuma akwai daga ãyõyinsa, jirãge mãsu gudãna a cikin tẽku kamar duwãtsu.
آية رقم 34

Kõ Ya halakã su (sũ jirãgen) sabõda abin da mãsu su suka sanã'anta, alhãli kuwa Yanã yãfe (laifuffuka) mãsu yawa.

Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci, kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai.

Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã ciyarwa.

Kuma Lalle ne, wanda ya nẽmi taimakon rãmãwa a bãyan an zãlunce shi, to waɗannan bãbu wata hanyar zargi a kansu.
آية رقم 43

Kuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya gãfarta (wa wanda ya zãlunce shi), to shĩ wancan aiki haƙĩƙa, yanã daga manyan al'amura (da Allah ke so).

Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩnMu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya.
تقدم القراءة