ترجمة سورة عبس

Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
ترجمة معاني سورة عبس باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation .

Abasa


Yã game huska kuma ya jũya bãya.

Sabõda makãho yã je masa.

To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.

Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?

Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.

Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!

To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?

Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.

Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.

Kai kuma kã shagala ga barinsa!

A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.

Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).

(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,

Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.

A cikin hannãyen mala'iku marubũta.

Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.

An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!

Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).

Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.

Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.

Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).

To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.

Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.

Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.

Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.

Da inabi da ciyãwa.

Da zaitũni da itãcen dabĩno.

Da lambuna, mãsu yawan itãce.

Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.

Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.

To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.

Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.

Da uwarsa da ubansa.

Da mãtarsa da ɗiyansa.

Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.

Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.

Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.

Baƙi zai rufe su.

Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).
Icon