ترجمة معاني سورة الأنعام باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية

الترجمة الإنجليزية - صحيح انترناشونال
المنتدى الإسلامي
الترجمة الإنجليزية
الترجمة الفرنسية - المنتدى الإسلامي
نبيل رضوان
الترجمة الإسبانية
محمد عيسى غارسيا
الترجمة الإسبانية - المنتدى الإسلامي
الترجمة الإسبانية (أمريكا اللاتينية) - المنتدى الإسلامي
المنتدى الإسلامي
الترجمة البرتغالية
حلمي نصر
الترجمة الألمانية - بوبنهايم
عبد الله الصامت
الترجمة الألمانية - أبو رضا
أبو رضا محمد بن أحمد بن رسول
الترجمة الإيطالية
عثمان الشريف
الترجمة التركية - مركز رواد الترجمة
فريق مركز رواد الترجمة بالتعاون مع موقع دار الإسلام
الترجمة التركية - شعبان بريتش
شعبان بريتش
الترجمة التركية - مجمع الملك فهد
مجموعة من العلماء
الترجمة الإندونيسية - شركة سابق
شركة سابق
الترجمة الإندونيسية - المجمع
وزارة الشؤون الإسلامية الأندونيسية
الترجمة الإندونيسية - وزارة الشؤون الإسلامية
وزارة الشؤون الإسلامية الأندونيسية
الترجمة الفلبينية (تجالوج)
مركز رواد الترجمة بالتعاون مع موقع دار الإسلام
الترجمة الفارسية - دار الإسلام
فريق عمل اللغة الفارسية بموقع دار الإسلام
الترجمة الفارسية - حسين تاجي
حسين تاجي كله داري
الترجمة الأردية
محمد إبراهيم جوناكري
الترجمة البنغالية
أبو بكر محمد زكريا
الترجمة الكردية
حمد صالح باموكي
الترجمة البشتوية
زكريا عبد السلام
الترجمة البوسنية - كوركت
بسيم كوركورت
الترجمة البوسنية - ميهانوفيتش
محمد مهانوفيتش
الترجمة الألبانية
حسن ناهي
الترجمة الأوكرانية
ميخائيلو يعقوبوفيتش
الترجمة الصينية
محمد مكين الصيني
الترجمة الأويغورية
محمد صالح
الترجمة اليابانية
روايتشي ميتا
الترجمة الكورية
حامد تشوي
الترجمة الفيتنامية
حسن عبد الكريم
الترجمة الكازاخية - مجمع الملك فهد
خليفة الطاي
الترجمة الكازاخية - جمعية خليفة ألطاي
جمعية خليفة الطاي الخيرية
الترجمة الأوزبكية - علاء الدين منصور
علاء الدين منصور
الترجمة الأوزبكية - محمد صادق
محمد صادق محمد
الترجمة الأذرية
علي خان موساييف
الترجمة الطاجيكية - عارفي
فريق متخصص مكلف من مركز رواد الترجمة بالشراكة مع موقع دار الإسلام
الترجمة الطاجيكية
خوجه ميروف خوجه مير
الترجمة الهندية
مولانا عزيز الحق العمري
الترجمة المليبارية
عبد الحميد حيدر المدني
الترجمة الغوجراتية
رابيلا العُمري
الترجمة الماراتية
محمد شفيع أنصاري
الترجمة التلجوية
مولانا عبد الرحيم بن محمد
الترجمة التاميلية
عبد الحميد الباقوي
الترجمة السنهالية
فريق مركز رواد الترجمة بالتعاون مع موقع دار الإسلام
الترجمة الأسامية
رفيق الإسلام حبيب الرحمن
الترجمة الخميرية
جمعية تطوير المجتمع الاسلامي الكمبودي
الترجمة النيبالية
جمعية أهل الحديث المركزية
الترجمة التايلاندية
مجموعة من جمعية خريجي الجامعات والمعاهد بتايلاند
الترجمة الصومالية
محمد أحمد عبدي
الترجمة الهوساوية
الترجمة الأمهرية
محمد صادق
الترجمة اليورباوية
أبو رحيمة ميكائيل أيكوييني
الترجمة الأورومية
الترجمة التركية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
مركز تفسير للدراسات القرآنية
الترجمة الفرنسية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
مركز تفسير للدراسات القرآنية
الترجمة الإندونيسية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
مركز تفسير للدراسات القرآنية
الترجمة الفيتنامية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
مركز تفسير للدراسات القرآنية
الترجمة البوسنية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
مركز تفسير للدراسات القرآنية
الترجمة الإيطالية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
مركز تفسير للدراسات القرآنية
الترجمة الفلبينية (تجالوج) للمختصر في تفسير القرآن الكريم
مركز تفسير للدراسات القرآنية
الترجمة الفارسية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
مركز تفسير للدراسات القرآنية
Dr. Ghali - English translation
Muhsin Khan - English translation
Pickthall - English translation
Yusuf Ali - English translation
Azerbaijani - Azerbaijani translation
Sadiq and Sani - Amharic translation
Farsi - Persian translation
Finnish - Finnish translation
Muhammad Hamidullah - French translation
Korean - Korean translation
Maranao - Maranao translation
Abdul Hameed and Kunhi Mohammed - Malayalam translation
Salomo Keyzer - Flemish (Dutch) translation
Norwegian - Norwegian translation
Samir El - Portuguese translation
Polish - Polish translation
Romanian - Romanian translation
Elmir Kuliev - Russian translation
Albanian - Albanian translation
Tatar - Tatar translation
Japanese - Japanese translation
محمد جوناگڑھی - Urdu translation
Ma Jian - Chinese translation
Turkish - Turkish translation
King Fahad Quran Complex - Thai translation
Ali Muhsin Al - Swahili translation
Abdullah Muhammad Basmeih - Malay translation
Hamza Roberto Piccardo - Italian translation
Indonesian - Indonesian translation
Bubenheim & Elyas - German / Deutsch translation
Bosnian - Bosnian translation
Hasan Efendi Nahi - Albanian translation
Sherif Ahmeti - Albanian translation
Sahih International - English translation
Czech - Czech translation
Abul Ala Maududi(With tafsir) - English translation
Tajik - Tajik translation
Alikhan Musayev - Azerbaijani translation
Muhammad Saleh - Uighur; Uyghur translation
Abdul Haleem - English translation
Mufti Taqi Usmani - English translation
Muhammad Karakunnu and Vanidas Elayavoor - Malayalam translation
Sheikh Isa Garcia - Spanish; Castilian translation
Divehi - Divehi; Dhivehi; Maldivian translation
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Mahmud Muhammad Abduh - Somali translation
Knut Bernström - Swedish translation
Jan Trust Foundation - Tamil translation
Mykhaylo Yakubovych - Ukrainian translation
Uzbek - Uzbek translation
Diyanet Isleri - Turkish translation
Ministry of Awqaf, Egypt - Russian translation
Abu Adel - Russian translation
Burhan Muhammad - Kurdish translation
Dr. Mustafa Khattab, The Clear Quran - English translation
Dr. Mustafa Khattab - English translation
الترجمة الإنجليزية - مركز رواد الترجمة
الترجمة الفرنسية - محمد حميد الله
الترجمة الجورجية
الترجمة البوسنية - مركز رواد الترجمة
الترجمة الصربية - مركز رواد الترجمة - جار العمل عليها
الترجمة الألبانية - مركز رواد الترجمة - جار العمل عليها
الترجمة اليابانية - سعيد ساتو
الترجمة الفيتنامية - مركز رواد الترجمة
الترجمة التاميلية - عمر شريف
الترجمة السواحلية - عبد الله محمد وناصر خميس
الترجمة اللوغندية - المؤسسة الإفريقية للتنمية
الترجمة الإنكو بامبارا - ديان محمد
الترجمة العبرية
الترجمة الإنجليزية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
الترجمة الروسية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
الترجمة البنغالية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
الترجمة الصينية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
الترجمة اليابانية للمختصر في تفسير القرآن الكريم
ترجمة معاني القرآن الكريم - عادل صلاحي
عادل صلاحي

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske*, sa'an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.
____________________
* Duffai na dare da zãlunci da bin hukunce-hukuncen al'ãdu, haske kuma shĩ ne na taurãri da wuta da shari'u na Littãfi da annabci.
Sabõda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu.
Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce: "Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne."
Suka ce: "Don me ba a saukar da wani malã'ika ba a gare shi?" to dã Mun saukar da malã'ika haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin* sa'an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba.
____________________
  * Dã an hukunta al'amari da halakarsu, dõmin idan malã'ika ya sauka ga mutãnen da ake yi wa wa'azi bayyane, to, halakarsu tã je ke nan.
Kuma dã Mun sanya malã'ika ya zama manzo lalle ne dã Mun mayar da shi mutum, kuma dã Mun rikita musu abin da suke rikitãwa.
"Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne, (Allah) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya."
Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki."
Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa* kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.
____________________
* Yahũdu da Nasãra sunã sanin Annabi Muhammadu tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da abin da ya zo da shi na Alƙur'ãni, kamar yadda suka san ɗiyan tsatsõnsu; kamar yadda Abdullahi ɗan Sallãmi ya ce wa Umar: "Lalle ne na san shi a lõkacin da na gan shi, kamar yadda nake sanin ɗãna, kuma lalle ne, ni, mãfi tsananin sani ne ga Muhammadu fiye da ɗãna.".
Kuma rãnar da Muka tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki: "Inã abõkan tãrayyarku waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?"
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."
Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu ƙaryata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai."
Ã'aha, abin da suka kasance suna ɓõyẽwa, daga gabãni, ya bayyana a gare su. Kuma dã an mayar da su, lalle dã sun kõma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an ƙaryata manzanni daga gabãninka, sai suka yi haƙuri a kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cũtar da su, har taimakonMu ya je musu, kuma babu mai musanyãwa ga kalmõmin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da kai) ya zo maka daga lãbãrin (annabãwan) farko.
"Ã'a, Shĩ dai kuke kira sai Ya kuranye abin da kuke kira zuwa gare Shi, idan Ya so, kuma kunã mantãwar abin da kuke yin shirkin tãre da shi."
To, don me, a lõkacin da tsananinMu ya jẽ musu ba su yi tawãlu'i ba? Kuma amma zukatansu sun ƙẽƙashe kuma shaiɗan yã ƙawãta musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Sa'an nan kuma alõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũɗe, a kansu, ƙõfõfin dukkan kõme, har a lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yi tsuru tsuru.
آية رقم 49
Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, azãba tanã shãfar su sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.
Kuma kada ka kõri waɗanda* suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.
____________________
* Musulunci addinin Allah ne, wanda yake faƙĩrin dũkiya da mawãdãcinta, duka ɗaya suke a gare shi. Sabõda haka wanda duka ya rigayi wani a cikinsu, to, bã za a kõre shi ba dõmin ɗayan ya shiga. Allah ĩmãni Yake so, kõ daga wãne irin mutum yake, bã Ya bukãtar dũkiya.
آية رقم 55
Kuma kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, kuma dõmin hanyar mãsu laifi ta bayyana.
Ka ce: "Lalle ne, dã a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugãwa da shi, haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin, a tsakãnina da tsakãninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga azzũlumai."
Kuma a wurinSa mabũdan* gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa.
____________________
* Lõkacin aukuwar abũbuwa na alheri da na azãba da rãyuwa da mutuwa da sauransu, bãbu wanda ya san su sai Allah. Wanda ya ce ya san wani abu na gaibi alhãli kuwa shĩ ba wani manzon Allah ba, to, kãfiri ne. haka kuma wanda yake cewa, Annabãwã sun san dukkan gaibi, kamar yadda Allah Ya sani, shĩ mã kãfiri ne.
Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar* rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
____________________
* Karɓar rai da dare dõmin barci, tãyarwa a cikin ranã, watau yini daga barci. Akwai misalta dare da dũniya kuma rãna da Rãnar Ƙiyãma, kuma mutuwa da barci, da farkawa daga barci da Tãshin Ƙiyãma. Ãyar tã ƙunsa asĩrai mãsu yawa.
Ka ce: "Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kunã kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓõye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan (masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga mãsu gõdiya?'"
Kuma babu wani abu daga hisãbinsu (mãsu kutsãwa a cikin ayõyin Allah (a kan mãsu taƙawa amma akwai tunãtarwa (a kansu), tsãmmãninsu (mãsu kutsawar) zã su yi taƙawa.
Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wãsa* da wargi alhãli rãyuwar dũniya tã rũɗe su, kuma ka tunãtar game da shi (Alƙur'ãni): Kada a jẽfa raia cikin halaka sabõda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai cẽto; kuma, kõ ya daidaita dukan fansa, ba zã a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammãni sabõda abin da suka tsirfanta; sunã da wani abin shã daga ruwan zãfi, da wata azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
____________________
* Suka sanya sãbabbin abũbuwa a cikinsa, waɗanda suke bãbu su a cikinsa, kamar Khawãrijãwa da sãshen wanda ke da'awar danganuwa zuwa ga sãlihai inda suka sanya Ɗarĩka mai sãdarwa zuwa ga Allah, bandiri da algaita, kuma suka fãra abũbuwa waɗanda ba su halatta ba ga shari'a. Daga Sãwĩ. 
Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'"* Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai."
____________________
* Shi kuma bã ya karɓãwa balle ya nufi wurin shiriyar da suke kiran sa ya tafi, sabõda yã riga yã fãɗi daga sama zuwa ƙasa, kuma ɗimuwa tã kãmã shi.
"Kuma (an ce mana): Ku tsai da salla kuma ku bĩ shi (Allah) da taƙawa kuma Shi ne wanda Yake zuwa gare Shi ake tãra ku."
Kuma kamar wancan ne, Muke nũna wa Ibrãhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dõmin ya kasance daga mãsu yaƙĩni.
Sa'an nan a lõkacin da ya ga rãnã tanã bayyana, ya ce: "Wannan shĩ ne Ubangijina, wannan ne mafi girma?" Sa'an nan a lõkacin da ta fãɗi, ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki."
Kuma daga ubanninsu, da zũriyarsu, da 'yan'uwansu, kuma Muka zãɓe su, kuma Muka shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lõkacin da suka ce: "Allah bai saukar da kõme ba ga wani mutum." Ka ce: "Wãne ne ya saukar da Littãfi wanda Mũsã ya zo da shi, yanã haske da shiriya ga mutãne, kunã sanya shi takardu, kũna bayyana su, kuma kunã ɓõye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah,"* sa'an nan ka bar su a cikin sharhõliyarsu sunã wãsã.
____________________
  * Allah ne Ya saukar da shi, sabõda haka ba zai zama abin mãmãki ba ko abin musu ga Ya saukar da wani littãfi kamar Alƙur'ãni ga wani mutum a bãyan Taurãta ga Musã. Kuma a cikin Taurãtar ba a ce ita ce ƙarshen Littãfin Allah ba kuma Mũsã bã shi ne ƙarshen Annabawa ba.
Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda yake a gabansa ne, kuma dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda yake gefenta. Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da Lãhira sunã ĩmãni da shi (Alƙur'ãni), kuma sũ, a kan sallarsu, sunã tsarẽwa.
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai."
Kuma lalle ne haƙĩƙa, kun zo Mana ɗai ɗai, kamar yadda Muka halittã ku a farkon lõkaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma ba Mu gani a tãre da kũ ba, macẽtanku waɗanda kuka riya cẽwa lalle ne sũ, a cikinku mãsu tãrayya ne. Lalle ne, hãƙĩƙa, kõme yã yanyanke a tsakãninku, kuma abin da kuka kasance kunã riyãwa ya ɓace daga gare ku.
Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai,* wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?
____________________
* Mai ĩmãni daga kãfiri kõ kãfiri daga mai ĩmãni, da mai arziki daga matalauci da matalauci daga mawadãci, sarki daga talaka da talaka daga sarki,da mai sanyi daga mai zãfi ko mai zãfi daga mai sanyi, haka dai ga kõme Allah Yanã fitar da kĩshiyarsa. 
Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren),* kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni.
____________________
* Allah na halitta kõren ganye daga hasken rãnã, sa'an nan Ya halitta gãrin ƙwãyã daga kõren. 
Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa.
Mafarin* halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?
____________________
* Shi ne wanda Ya fãri halittarsu bã da Yã kõya daga wani ba. Sautin jan wasalin fa zaiyi sama dõmi bambanci daga mafãri watau sababin abu, ana mĩƙe sautin maddi a gare shi.
آية رقم 105
Kamar wannan ne Muke sarrafa ãyõyi, kuma dõmin su ce: "Kã karanta!" Kuma dõmin Mu bayyana shi ga mutãne waɗanda sunã sani.
Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwõyinsu (cẽwa) lalle ne idan wata ãyã ta jẽmusu, haƙĩƙa, sunã yin ĩmãni da ita. Ka ce: "Abin sani kawai, ãyõyi a wurin Allah suke. Kuma mẽne nezai sanya ku ku sansance cẽwa, lalle ne su, idan ãyõyin sun je, ba zã su yi ĩmãni ba?"
Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra* zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa.
____________________
* Wahayin shaiɗãnu sãshensu zuwa ga sãshe da ƙãwata ƙarya ta zama kamar gaskiya. Kamar Shaiɗan ya sanya wasiwãsi: Dã da'awar Annabi gaskiya ce: Ai dã manyan mutãne ne zã su fãra bin ta, ba matalautã ba, kõ kuwa annabi mai sihiri ne dõmin yanã raba miji da mãta, da ɗa da uba. Watau su karkatar da magana, dõmin su karkatar da wãwãye daga bin gaskiya. 
Kuma dõmin zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata.
Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi (Alƙur'ãni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakka.
Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya* da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.
____________________
* Musulunci kõ Alƙur'ãni ne cikon addinin Allah, babu mai iya zõwa da wani abu sãbo kõ ya ƙãra wani abu a cikin sa ta kõwace hanya kuma bãbu mai iya musanya wani abu a cikinsa. Ya cika ya kammala, sai biya kawai. Annabi ya ce: "Wanda ya yi wani aiki ba da umuruinsa a kan abin da ya aikata ɗin nan ba, to, an mayar masa; ba a karɓaba.". 
Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah. Ba su bin kõme sai fãce ƙaddari-faɗi* suke yi.
____________________
 * Kamar maganarsu cewa mũshe wanda Allah da kansa Ya kashe, ya fi dã cewa da a ci shi, bisa ga abin da mutãne suka yanka. 
Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah* kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa.
____________________
* An sani daga nan cewa ambaton sũnan Allah wajen yankan dabba wãjibi ne, idan an tuna. Wanda ya manta, anã cin yankansa, amma wanda ya bari da gangan, bã zã a ci yankansa ba.
Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa.* Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne.
____________________
* Sabõda haka bã a cin yankan majũsu. Anã cin yankan bakitãbe, babu ruwanmu da abin da yake faɗa, tun da Allah Ya halatta mana cin abincinsu alhãli kuwa Ya san sun riga sun musanya addininsu. Idan Musulmi ya bar sũnan Allah da gangan, amma bai ambaci sũnan kõwa ba, to, akwai riwãya biyu game da haka, ci kõ rashin ci. Amma idan ya haɗa sũnan Allah da na wani, to, ba zã a ci ba, dõmin yã yi ridda. 
Kuma kamar wancan ne Mun sanya a cikin kõwace alƙarya, shugabanni sũ ne mãsu laifinta dõmin su yi mãkirci a cikinta, alhãli kuwa ba su yin makirci fãce ga rayukansu, kuma ba su sansancẽwa.
Kuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: "Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa.* Wani wulaƙanci** a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi waɗanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci.
____________________
* Manzanci da zãɓin Allah yake, bã da kuɗi kõ'ya'ya kõ kabĩla yake ba, sai a wurin da Allah Ya aza shi.  ** Mai girman kai ga bin umurnin Allah, sakamakonsa wulaƙanci ne.
Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa* ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni.
____________________
* Mai tãkãwa zuwa sama ƙirjinsa ƙunci yake yi, sabõda iskar numfashi tanã raguwa gare shi. Kuma shi yanã shasshekar gajiya da rashin iska. Wannan ilmi yanã a cikin mu'ujizar Alƙur'ani. 
Wannan ita ce hanya ta Ubangijinka madaidaiciya. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki ga mutãne mãsu karɓar tunãtarwa.
Kuma rãnar da yake tãra su gaba ɗaya (Yanã cẽwa): "Yã jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne." Kuma majiɓantansu daga mutãne suka ce: "Yã Ubangjinmu! Sãshenmu* ya ji dãɗi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!" (Allah) Ya ce: "Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani."
____________________
* Haka dai mai laifi a bãyan azãbar laifinsa ta tabbata a kansa bã ya ɓõyewar abin da ya riga ya bayyanã, sai ya faɗa da kansa dõmin ya bayyanar da nadãmarsa a lõkacin da nadãma bã ta da amfãni
آية رقم 129
Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa.
Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.*
____________________
* Allah bã Ya halaka mutãne sabõda wani laifi, sai bãyan Ya aiki mai gargaɗi ya tafi ya yi musu gargaɗi, sun san laifinsu, sun ƙi bari, sa'an nan azãba ta je musu.
Kuma ga kõwanne,* akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.
____________________
* Kõwace jama'a, ta mãsu ɗã'a da ta mãsu sabõ, sunã da sakamakõ gwargwadon matsayin kõwanne, ga ĩmãninsa da aikinsa kõ kuwa kãfircin sãɓonsa.
Kuma Ubangijinika Wadãtacce* ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.
____________________
 * Rashin gaugãwar yin sãkamako ga mãsu laifi sabõda wadãtar Allah ne. Bã shi yin uƙũba dõmin Ya yi fushin an rage masa mulki, haka kuma bã shi yin ni'ima domin an ƙãra masa mulki. Sai dai dõmin Ya nũna ãdalci da falala ne kawai.
Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: "Wannan* na Allah ne," da riyãwarsu "Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne." Sa'an nan
____________________
 * Sun kasance a cikin  jahiliyya idan suka yi nõma kõ kuwa idan suka sami 'ya'yan itace, sai su sanya wani juz'i daga gare shi ga Allah, wani juz'i kuma ga gumãka. Abin da yake rabon gumaka, sai su tsare shi, kuma su lissafce shi. Idan wani abu ya fãɗi daga abin da aka ambace shi ga Samad, sai su mayar da shi zuwa ga rabõn gumãka, amma rabõn gumãkan, bã ya zuwa ga na Allah. Anã bayãr da rabon Allah ga miskĩnai, kuma rabõn gumaka ga matsaransu.
Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar* 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.
____________________
* Sunã turbuɗe 'ya'ya mata, dõmin tsõron talauci kõ dõmin tsõron kunya. Sai mai haihuwa ta haihu a bãkin rãmi, idan mace ta haifa, sai ta tũra ta cĩkin rãmin ta rufe, idan kuma namiji ne sai ta bar shi. Haka kuma kashe 'ya'ya, a kan bãkance da alwãshi, sunã ganin sa ibada ne.
Kuma daga rãƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, dõmin ya ɓatar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Ka ce: "Bã ni sãmu,* a cikin abin da aka yõ wahayi zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
____________________
   * Bayãnin abũbuwan da aka haramta cinsu daga dabbõbi waɗanda Allah Ya hana, bã waɗanda al'ãda ta hana ba.
Kuma a kan waɗanda suka tũba (Yahũdu) Mun haramta *dukan mai akaifa, kuma daga shãnu da bisãshe Mun haramta musu kitsattsansu fãce abin da bãyukansu suka ɗauka, kõ kuwa kãyan ciki, kõ kuwa abin da ya garwaya da ƙashĩ wannan ne Muka sãka musu sabõda zãluncinsu, kuma Mu, haƙĩƙa, Mãsu gaskiya ne.
____________________
   * Bayãnin abũbuwan da Allah Ya hana a kan Yahũdu, shi ma hanin an yĩ shi sabõda wani laifinsu ne.
Waɗanda suka yi shirki* zã su ce: "Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi."
____________________
 * Wahayin shaiɗan zuwa ga mãsu shirki da hana dabbõbi da ƙãga wasu hukunce-hukunce. Kalmar gaskiya ce ake yin nufin ƙarya da ita, da bãyanin warware rikicin. Jũyar da maganar gaskiya dõmin a yi ƙarya da ita yanã sabbaba saukar azãba. Kuma dukan maganar da bã ta da asali ga Littãfi kõ sunna, to, bã gaskiya ba ce, bin ta nau'in shirki ne.
Ka ce: "Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta." wãjibi ne a kanku kada ku yi shirkin kõme da Shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatãwa, kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su, kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammãninku, kunã hankalta.
Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa.
Sa'an nan kuma Mun bai wa Mũsã Littãfi, yanã cikakke bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah) da rarrabẽwa, daki-daki, ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu,* sunã yin ĩmãni da haɗuwa da Ubangijinsu.
____________________
* Mabiya Littãfin Mũsã watau Yahũdu, idan sun san cewa Alƙur'ãni kamar Attaura yake daga Allah aka saukar da shi, kuma Muhammadu Annabin Allah ne kamar Mũsã kuma sũ duka suna gaskata jũnã, sai su ji sauƙin ĩmãni da shi.
آية رقم 155
Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.
(Dõmin) kada ku ce: "Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan ƙungiya* biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance, daga karatunsu, haƙĩƙa, gãfilai."
____________________
 * Ana magana da mãsu shirkin Larabawa, ƙungiyõyin biyu kuwa su ne Yahũdu da Nasãra, littãfin shĩ ne Attaura da Linjĩla.
Kõ kuwa ku ce: "Dã dai lalle mũ an saukar da Littãfi a kanmu, haƙĩƙa, dã mun kasance mafiya, shiryuwa daga gare su." To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, tã zo muku, da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Zã Mu sãka wa waɗanda suke finjirẽwa daga barin ãyõyinMu da mugunyar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na hinjirẽwa.
Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku* su je musu kõ kuwa Ubangijinka Ya je, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka ya je. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka yake zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba a gabãni, kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri, bã ya amfãninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne."
____________________
 * Zuwan malã'iku dõmin karɓar rãyukansu, zuwan Allah dõmin yin hisãbin bãyi, zuwan sãshen ãyõyin Ubangiji shĩ ne fitõwar rãnã daga yamma da fitar Rãƙumar Sãlihu. Waɗannan abũbuwa duka idan sun auku a kan wanda bã shi da imani a gabãnin aukuwarsu, kuma ya zama yã aikata ayyukan alheri da shari'a ta umurce shi da yi, to, bã za a karɓi wani ĩmãninsa ba.
Lalle ne waɗanda* suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
____________________
  * Bãyan bayãnin wanda bai yi ĩmani ba sai bayãnin sababin rashin karɓar ĩmãnin ya zo, sai kuma ya ci gaba da bayãnin cewa, kõ wanda ya yi ĩmãnin idan yã ƙãra wasa abũbuwa a cikin addĩni bisa ga abin da Allah Ya saukar, ta haka har mutane suka zama ƙungiya ƙungiya, kamar mãsu ɗarĩƙõƙi na tasawwufi, to, su ma Annabi bã ya tãre da su ga kõme dõmin sun kõma wa hanyar jahiliyya a lõkacin da wasu suke ƙãga hukunce-hukunce a kan mutãne, suka zama da yin haka nan abũbũwan bautãwa, kuma mãsu bin su suka zama mushirikai. Daga nan har zuwa ga ƙarshen sũrar duka ta'lĩƙi ne ga dukan abin da sũrar ta ƙunsa na tauhĩdin Rubũbiyya da taƙaitãwa ga bãyanin muhimman mas'alolin da ta ƙunsa. Saninta shi ne rũhin addini.
Ka ce: "Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni, ƙĩmantãwa (ga abũbuwa), mai aƙĩdar Ibrãhĩm, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
"Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya ku mãsu maye wa jũnaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sãshenku bisa ga sãshe da darajõji; dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku." Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggãwar uƙkũba ne, kuma lalle ne Shi, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
تقدم القراءة