ترجمة سورة يس

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة يس باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Y. S̃.
Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni* Mai hikima.
____________________
   * Al-ƙur'ãni ma'anarsa abin karãtu. 
Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni.
A kan hanya madaidaiciya.
(Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne.
Lalle, haƙĩƙa, kalma* tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.
____________________
 * Kalma a nan ita ce faɗar Allah da take cewa zai yi azãba ga kãfirin da bai yi ĩmãni ba.
Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne.
Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani.
Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba.
Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci.
Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.
Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni* suka jẽ mata.
____________________
  * Su Manzannin Ĩsã ne zuwa Antãkiya, bãbban garin kasar Rũmu. Sũ ne Yõhana da Pulis. Na uku, shĩ ne sham'ũn. Mutumin da ya jħ yanã gaggawa, shi ne Habĩb Masassaki wanda ya fãra gamuwa da Manzannin farko, ya yi ĩmãni da su, sa'an ya jħ yanã wa'azi ga mutãnensa. 
A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku."
Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi."
Suka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku."
"Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne."
Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku."
Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi."
Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan.
"Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne."
"Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?"
"Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã."
"Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna."
"Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni."
Aka ce *(masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani."
____________________
 * An ce masa haka a bayan mutãne sun kashe shi sabõda ĩmãninsa. Wannan shi ne sakamakon mai wa'azi idan ya yi shahada a kan aikinsa na wa'azi.
"Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama."
Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama* a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba.
____________________
   * Wãtau halakar da su abu ne mai sauƙi a gare Mu, ba Mu yi bukãtar saukar da wasu sõjõjin malã'iku daga samã ba.
Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu.
Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili.
Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba?
Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu.
Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci.
Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta.
Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba?
Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba.
Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu.
Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani.
Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa.
Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo.
Kuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lõdi.
Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa.
Kuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su, kuma ba su zama anã tsirar da su ba.
Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan lõkaci.
Kuma idan aka ce musu, "Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku."
Kuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã mãsu bijirẽwa daga gare ta.
Kuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, "Ashe, zã mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya."
Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance mãsu gaskiya?"
Bã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma.
Bã zã su iya yin wasiyya* ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba.
____________________
* Mãsu izgili ga addini idan ajali ya je musu bisa ga abke, bã zã a bã su dãmar wasiyya ba ga iyãlansu.
Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu.
Suka ce: "Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya."
Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu.
To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi.
Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira.
Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo.
"Aminci," da magana,* daga Ubangiji Mai jin ƙai.
____________________
 * Ana ce musu aminci ya tabbata a gare ku, da magana daga wajen Ubangijinsu Mai rahama, watau ana fada musu haka da magana bã da wata ishãra ba. 
"Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!"
"Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?"
"Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya."
"Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?"
"Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita."
"Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."
A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Dã Mun so, dã Mun shãfe gani *daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani?
____________________
 * Dã Mun so shãfe ganinsu na ido kamar yadda Muka shãfe basĩrarsu ta hankali, dã Mun shãfe shi, sai su zama makãfin idãnu kamar yadda suke makãfin zũci. Sabõda haka ko sun so gani, bã zã su yi ba.
Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba.
Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta?
Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne.
Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai.
Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su?
Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci.
Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba?
Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su.
Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wutã).
Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa.
Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar.
Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu?"
Ka ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne."
"Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi."
"Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne, Mai ilmi."
UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).
Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
Icon