ترجمة سورة المعارج

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة المعارج باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
Daga Allah Mai matãkala.
Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
Da matarsa da ɗan'uwansa.
Da danginsa, mãsu tattarã shi.
Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
Mai twãle fãtar goshi.
Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
Sai mãsu yin salla,
Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!
Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?
A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).
Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)
Icon