ترجمة سورة مريم

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة مريم باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

K̃.H. Y.I. Ṣ̃.
Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.
A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye.
Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!"
"Kuma lalle nĩ, na ji tsõron* dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa."
____________________
 * Amfãnin sãmu ɗã ga mutumin kirki shi ne dõmin ya gãji kirkin kuma ya taimaki sauran danginsa, ya rãyar da gida. Kuma wanda ba mutumin kirki ba yana yiwuwa ya sãmi ɗan kirki mai shiryar da shi zuwa ga hanyar ƙwarai.
"Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!"
(Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni."
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?"
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba."
Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai."
Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma."
Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro.*
____________________
  * Yahaya an zakariyya, shi neAnnabi da aka bai wa hukunci tun yanã yãro. Kuma Shĩ ne mai bãyar da bushãra da Ĩsa, amincin Allah ya tabbata agare su.
Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa.
Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba.
Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai.
Kuma ka ambaci Maryamu* a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
____________________
  * An fãra da ƙissar Maryamu dõmin a nũna sakamakon da aka yi mata da sãmun ɗan kirki sabõda kasancewarta mutumiyar kirki, kuma da nũna cewa Annabi Ĩsa bã ɗan Allah ba ne.
Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.
Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!"
Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki."
Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?"
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi* ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce."
____________________
 * Malã'ikin da ya je ga Maryama a cikin sũrar mutum jibrĩlu ne Yã hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi ciki da Ĩsa.
Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.
Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"
Sai (yãron da ta haifa) ya* kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.
____________________
 * Annabi Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya fãra magana ga uwarsa tun a lõkacin da aka haife shi yanã a ƙarƙashin uwarsa. Gudãnar ruwan marmaro a ƙarƙashinta da fitar da 'ya'yan dabĩno dagakututturen dabĩno, alãmu ne mãsu nũna cħwa Allah nã iya halitta jãrĩri bã da uba ba, kuma Yanã tãyar da matattu daga kabarinsu bã da wata wahala ba.
"Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu."
"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki*. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."
____________________
   * Jin sanyi ga idãnu shĩ ne farin cikin sabõda sãmun haihuwa. Ga ibãdar Banĩ lsrã'ĩla, mai azumi bã ya yin magana, amma ga Musulunci Allah Ya shãfe wannan hukunci. Mai azumi yanã magana sai dai anã son ya kãma bãkinsa daga maganar da bã ta ibãda ba.
Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!
"Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba."
Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?"
Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."*
____________________
 * Wannan ita ce maganar da Ĩsa ya yi wa mutãnen uwarsa dõmin ya barrantar da ita daga tuhuma, kuma ya nũna matsayinsa ga Allah da muƙãminsa na Annabci.
"Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai."
"Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."
"Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai."
Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.
Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã*. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.
____________________
 * Ba ya kasancewa ga Allah Ya riƙi ɗã, dõmin bã Ya mutuwa balle Ya yi bukãtar mai gãdo ga tsaron dũkiya. Shi kaɗai ne, bã Ya bukãtar wani ɗã mai tsaron dangi dõmin kada su bar hanya.
"Kuma lalle Allah ne Ubangijina* kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."
____________________
 * Tana a cikin maganar Ĩsã a lõkacin da ya girma yana wa'azi ga mutãnensa, sabõda haka aka raba ta da maganar farko a lõkacin da yake jãrĩri.
Sai ƙungiyõyin(5) suka sãɓã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.
____________________
 (5) Bãyan ɗauke Annabin Allah Ĩsã ɗan Maryama ƙungiyõyin mutãne sun sãɓa wa jũnansu a cikin sha'aninsa. Yahũdu suna sũkar sa, Nasãra suka kasu uku: Nasũriyya suka ce: "Shi ɗan Allah ne" Malakaniyya suka ce: "Shi ne na uku ɗin uku," Ya'aƙũbiyya suka ce: "Shi ne Allah." Sabõda haka Nasara sukahaihaye kuma suka zurfafa, sa'an nan Yahũdu suka taƙaita kuma suka yi sũka gare shi.
Mẽne ne ya yi jinsu(6), kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.
____________________
 (6) A rãnar Lãhira a lõkacin da ake yi musu hisãbi a gaban Allah ganinsu da jinsu sunã da kyau ƙwarai, amma a nan dũniya sunã a cikin makanta da kurumci sabõda ɓatar da suka yi, suka ƙaryata Ĩsã, aminci ya tabbata a gare shi.
Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni.
Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa* da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.
____________________
 *Tun da yake Mũ ke gãdon ƙasa da wanda yake a cikinta,bã zã Mu yi bukãtar sãmun wani magãji ba.
Kuma ambaci Ibrãhĩm* a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
____________________
  * Ibrãhĩm ya yi ƙõƙarin shiryar da ubansa, sai dai Allah bainufi shiryuwarsa ba. Daga cikin amfãnin haihuwa akwai abin haihuwa ya shiryar da mahaifinsa, ya yi masa nasĩha gwargwadon hãli.
A lõkacin da ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka?"
"Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici."
"Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama."
"Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan."
Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci."
Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka.* Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni."
____________________
 * Ibrãhĩm yã mayar da magana mai kyau da laushi da aminci ga maganar ubansa mai mũni da gautsi da tsõratarwa. Wannan yanã kõyar da yadda ake kira zuwa ga Allah da kuma yadda ya kamãta a tausasa wa uba kõ dã shi kãfiri ne.
"Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina."
To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi.
Kuma Muka yi musu kyauta daga RahamarMu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya* maɗaukaki.
____________________
* Harshen gaskiya, shi ne yabo mai kyau daga Allah da mutãne. Wanda ya yankewa mutãnenSa dõmin Allah, to, zai sãka masa da waɗansu mutãnen kirki dõmin su ɗebe masa kewa.
Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa.
Kuma Muka yi masa kyauta daga RahamarMu da ɗan'uwansa Hãrũna, ya zama Annabi.
Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens *da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.
____________________
   * Mãtarsa da 'ya'yansa da Jurhum, yanã umurninsu da salla da zakka. Yanã wajaba ga mutum ya umurci iyalinsa da tsare haƙƙõƙin Allah.
Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki.
Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka.
Sai waɗansu 'yan bãya* suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri.
____________________
  * An ruwaito cewa wannan zai auku a lõkacin Tãshin Ƙiyãma ne a bãyan tafiyar sãlihan wannan al'umma ta Muhammadu. Zã su dinga barbarar jũnansu a cikin hanyõyi. Su tõzarta salla, su gina manyan gidãje su hau dukan abin da aka hana su, su tufanci abin da aka hana su, Ƙurɗabi.
Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme.
Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa.
Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice.
Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa.
(Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka* Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma** (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.
____________________
  * 'Yan Aljanna sunã cewa ba mu sauka a waɗannan gidãje ba sai da umurnin Ubangijinka, kai mai karatu, A1lahne Mai mallakar kõme, kuma kõme ãyã ne mai nũni zuwa gare shi, sabõda haka bã a mantãwa da shi. ** Maganar Allah ce a bãyan maganar 'yan Aljanna dõmin ta'aƙĩbi da ƙãrin bayãni ga maganarsu.
Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara a gare shi?
Kuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai?"
Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba?
To, Munã rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne.
Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya.
Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗanda suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita.
Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata.* Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce.
____________________
 * Idan an tãra mutãne dõmin hisabi, anã ajiye wuta a tsakãnin mutãne da Aljanna, Sa'annan a gitta sirãɗi a cikan wutar dõmin mutãne su bi akansa su ƙetare wutar zuwa Aljanna kuma waɗansu su fãɗa a cikin wutar dõmin azãba dawwamamma kõ kuma ta ɗan lõkaci gwargwadon laifi.
Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne.
Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?"
Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã.*
____________________
  * Kãyan ɗãki na jin dãɗi kamar gadãje da kujeri da kãyan cin abinci. Magãnã kuwa ita ce wurin da ake ganĩ ga mutum kamar tufãfinsa da sũrar jikinsa da dukan abin gani daga gare shi.
Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna!"
Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma.
Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?"
Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?
Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa.
Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai.
Kuma suka riƙi gumãka,* baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.
____________________
  * Gunki, shi ne dukan abin bautawa wanda bã Allah ba. Wanda ya riƙi wani sãlihi ko malã'iki ko aljani, yanã bauta masa, to, yã riƙe shi gunki ke nan. Bauta ita ce bin umurni da barin hani. Wanda ya bi umurnin da bã na Allah ba, kõ ya bar abin banin da ba na Allah ba, to, ya bauta wa mai umurnin ko mai hanin, yã riƙe shi gunki baicin Allah.
Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.
Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu* a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?
____________________
  * Idan shaiɗanu sun ga mai wa'azin gaskiya, sai su dinga shũshũta mabiyansu dõmin su yi faɗa da mai wa'azin, dõmin kada su saurare shi har su gãne ɓatarsu. Shaidan shi ne mai ɓatar da wani, mutum ne kõ aljani.
Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar ajali ne kawai, ƙidãyãwa.
A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma.
Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa.
Ba su malakar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama.
Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã!"
Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni.
Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu.
Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama.
Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã.
Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã.
Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya.
Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai.
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so.*
____________________
   * Wanda ya bi Allah da gaskiya, Allah zai sanya zukãtan mutãne su sõ shi kamar yadda yake a cikin Hadisi wanda Imãm Tirmizi ya ruwaito daga sa'ad da Abu Huraira.
Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma.
Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu?
Icon