ترجمة سورة الإنشقاق

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة الإنشقاق باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Idan sama ta kẽce,
Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
To, zã shi dinga kiran halaka!
Kuma ya shiga sa'ĩr.
Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
Da dare, da abin da ya ƙunsa.
Da watã idan (haskensa) ya cika.
Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?
Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.
Icon