سورة يونس

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Yunus a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Waɗannan matattãrarsu Jahannama ce sabõda abin da suka kasance sunã tsirfãtawa.
Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabãninku, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, amma ba su kasance sunã ĩmãni ba. Kamar wannan ne, Muke sãkãwa ga mutãne mãsu laifi.
Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi.*" Ka ce: "Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma."
____________________
  * Sunã nufin idan ya musanya shi, su ce: " To, gã shi ka bayyana cewa kai ne mai ƙirƙira shi, kanã jinginã shi ga Allah.".
Kuma mutãne ba su kasance ba fãce al'umma guda, sa'an nan kuma suka sãɓã wa jũna, kuma ba dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, dã an yi hukunci a tsakãninsu a kan abin da yake a cikinsa suke sãɓã wa jũna.
Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya.
Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare kõ kuma da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗanda suke tunãni.
Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari)1), wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.
____________________
 * Mãsu aikin ƙwarai waɗanda suka karɓa kiran Allah sunã da sakamakon abu mai kyau, wãtau Aljanna, kuma da ƙãri, watau ganin Ubangijinsu a cikin Aljanna. Haka Hadisi ya yi fassara.
Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, "Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku." Sa'an nan Mu rarrabe a tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: "Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa ba."
"To, kuma Allah Yã isa zama shaida a tsakãninmu da tsakãninku. Haƙĩƙa mun kasance ba mu san kõme ba na bautãwarku a gare mu!"
Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi fãsiƙanci, cẽwa haƙĩƙa sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.
Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu alkawari, kõ kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makõmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatãwa.
Kuma ga kõwace al'umma akwai Manzo*. Sa'an nan idan Manzonsu ya je, sai a yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma sũ, bã a zãluntar su.
____________________
  * Manzo na farko shĩ ne mai shiryar da su, Manzo na biyu shi ne ajalinsu.
Shi ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku.
Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne.
To, Lalle ne masõyan* Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba.
____________________
* Waliyyin Allah, shi ne masõyin Allah da sharaɗin ya zama mumini mai taƙawa watau yanã aiki da abin da Allah Ya umurce shi, kuma yanã barin abin da Allah Ya hana shi, bisa harshen Annabinsa wanda yake biya. Bãbu ƙarin kõme bãbu ragi. Bushãrarsu, ita ce yabon mutãne a gare su, kõ kuma a lõkacin mutuwarsu malã'iku su riƙa yi musu bushãra da gamuwa da Ubangijinsu, kõ kuma a cikin kabari wajen tambaya. Allah ne Mafi sani. 
Verse 63
Waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa.
Kada maganarsu* ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani.
____________________
 * Maganarsu ta izgili a gare ka. Idan Allah Ya ɗaukakã ka, bãbu mai iya hanãwa dõmin Shi kaɗai ne Mai izza kuma sai inda Ya sanya ta ga wanda Ya so.
Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
"Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."*
____________________
* Watau dukan abin da na zo muku da shi na umurni kõ hani, to, ni ma an umurce ni da yinsa kõ barinsa. Kuma bã ni neman wata ijãrar karantarwa daga gare ku dõmin Allah Ya umarce ni da iyar da manzancinsa zuwa gare ku, sabõda haka Shi ne zai biyã ni tsãdar aikĩna.
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla*, kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni.
____________________
  * Su sanya gidãjensu sunã fuskantar Alƙibla ta Ka'aba dõmin su riƙa yin salla a cikin gidãjen, sabõda tsõron in sun tafi masallaci zã a fãɗa su da dũka sunã a cikin salla. Wannan kuma yã nũna yadda ake son gidajen Musulmi su kasance a kõ da yaushe. 
Sai MũSã ya ce: "Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar (damutãne) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri* a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi."
____________________
  * Mũsã ya yi addu'a a kansu, har da rashin ĩmãni sabõda yã sãmi lãbãrin bã zã su yi imãni ba, kamar mutãnen Nũhu.
Kuma Muka ƙẽtãrar da Banĩ Isrã'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zãlunci da ƙẽtare haddi, har a lõkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: "Nã yi* ĩmãni cẽwa, haƙĩƙa, bãbu abin bautawa fãce wannan da Banũ Isrã'il suka yi ĩmãni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi."
____________________
 * Ĩmãni a bãyan Manzon mutuwa ya isa ga kãfiri bã zai yi masa amfãni ba. 
Ashe! A yanzu! Alhãli kuwa, haƙĩƙa ka sãɓa a gabãni, kuma ka kasance daga mãsu ɓarna?
To, a yau Munã kuɓutar* da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu.
____________________
* Kuɓutar da jikin Fir'auna: Banda rũhinsa dõmin a tabbatar da yã mutu. 
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar* da Banĩ Isrã'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa mãsu dãɗi. Sa'an nan ba su sãɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Kiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna.
____________________
* Allah Yã bai wa Banĩ Isrã'ila mulkin Masar da falasɗĩnu gabã ɗaya a bãyan halaka Fir'auna da mutãnensa.
To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi* ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.
____________________
  * Alƙaryun da aka aika da Manzanni cikinsu, ba su yi ĩmãni duka ba fãce mutum ɗaya, kõ biyu a gabãnin halaka ta sãmi mutãnensu. Sai dai alƙaryar Yũnusa, ita kam tã ji tsõro, ta yi ĩmãni a gabãnin saukar azãba, sabõda haka suka tshĩra, ba a halaka garin bawatau Nĩnawa. Watau bãbu mai iya sãmun ĩmãni sai Allah Ya nufe shi da haka. Kõ da mai yin gargaɗin ya kan yiwu ya karkace, sai da tsarin Allah.
Sa'an nan kuma Munã kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da mãsu ĩmãni.
"Kuma (an ce mini): Ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka.
تقدم القراءة