سورة الصافات

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar As-Saffat a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Verse 1
Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
Verse 2
Sa'an nan mãsu yin tsãwa* dõmin gargaɗi.
____________________
 * Mãsu tsãwa, sũ ne Malamai mãsu sãmun ilmin wa'azi daga Annabãwa waɗanda ke karãtun abin tunãwa daga Allah Ubangijin sammai da ƙasa, Mai bãyar da haske ga rãnã, Mai haskaka taurari mãsu ƙãwãtar da samã kuma su tsare ta daga shaiɗanu. An siffanta rãnã da Annabãwa, Malamai da taurãri, ilmi da haske da sababin ƙawa da shiryarwa da kõrar mãsu ɓarna.
Verse 3
Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
Verse 12
Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
Verse 24
Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
Verse 32
"Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
Verse 34
Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
Verse 38
Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
Verse 42
'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
Verse 48
Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
Verse 52
Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"
"Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"
Verse 54
(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"
Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."
"Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."
To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
Verse 89
Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
Verse 90
Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
Verse 94
Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
Verse 96
"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
Verse 101
Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro *mai haƙuri.
____________________
  * Yãron da aka yi bushãra da shi a nan, shĩ ne Ismã'ĩla' sabõda abin da yake tafe a gaba wanda ya shãfi Is'hãƙa da sũnansa a bayyane yã nũna a nan bã shi ba ne. Watau Ismã'ĩla kawai ne.
Verse 107
Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
Verse 112
Kuma Muka yi masa bushãra* Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
____________________
   * Wannan sãbuwar bushãra da Is'hãƙa tanã nũna cewa bã shĩ ne wanda kissar yankã ta shãfa ba sabõda haka Isma'ĩla dai ne tabbas, mai ƙissar yankã. Sabõda haka Allah Ya sanya shi wata al'umma dabam' dõmin a sãka masa, sa'an nan aka sãkawa Ibrãhĩm da Is'hãƙa dõmin ya zama wata al'umma ta dabam,.
Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
Verse 116
Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
Verse 117
Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
Verse 118
Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
Verse 124
A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"
Verse 125
"Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"
Verse 127
Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
Verse 129
Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
Verse 134
A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
Verse 135
Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
Verse 137
Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
Verse 141
Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
Verse 142
Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
Verse 145
Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
Verse 148
Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
Verse 149
Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"
Verse 152
"Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
Verse 159
Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
"Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,* fãce yanã da matsayi sananne."
____________________
  * Malã'iku da sauran halitta duka kõwa yã san matsayinsa na bauta ga Allah wanda ba Ya da dã ko diya, kuma ba Ya da dangantaka da kõwa. 
Verse 165
"Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
Verse 166
"Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
Verse 169
"Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
Verse 172
Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
Verse 175
Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.*
____________________
* Wannan ƙãrin bayãni ne ga abin da sũrar ke karantarwa na cewa Annabãwa sũ ne kamar rãna mai haske na asali. Mãlamai kamar taurãri suke mãsu sãmun haske daga rana su wãtsa ga dũniya kuma su kõre ɓarna. Aya ta l79 da ke tafe karfafawa ce ga ma'anar wannan.
Verse 176
Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
Verse 179
Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
تقدم القراءة