Fassarar Surar As-Sarhi a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية
Verse 1
ﯝﯞﯟﯠ
ﯡ
Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
Verse 2
ﯢﯣﯤ
ﯥ
Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
Verse 3
ﭑﭒﭓ
ﭔ
Wanda ya nauyayi bãyanka?
Verse 4
ﭕﭖﭗ
ﭘ
Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
Verse 5
ﭙﭚﭛﭜ
ﭝ
To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
Verse 6
ﭞﭟﭠﭡ
ﭢ
Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
Verse 7
ﭣﭤﭥ
ﭦ
Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
Verse 8
ﭧﭨﭩ
ﭪ
Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.
تقدم القراءة