سورة الجاثية

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Al-Jasiyah a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Lalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi* ga mãsu ĩmãni.
____________________
   * Ãya, ita ce alãma mai jan hankalin mutum zuwa ga shiriya. Jam'inta, shi ne ãyõyi.
Verse 7
Bone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi.
Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, *dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
____________________
   * Kwanukan Allah, sũ ne masĩfu waɗanda ke sãmun kãfirai waɗanda bã su bin sharĩ'ar Allah. Wãtau Allah Ya umurci Annabi ya gaya wa Musulmi, cewa wanda bã ya tsõron masĩfu sabõda ya ki aiwatar da sharĩ'ar Allah a kansa to kada Musulmi su dãmu da shi, watau kãfiran amãna nã iya bin dõkõkinsu na al'ãda, bãbu ruwan Musulmi matuƙar dai ba su shũka wata fitina ba a gare su. A bãyan haka Allah zai sãka wa kõwa game da aikinsa.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai* (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu).
____________________
 * Bã Musulmi kawai aka aikowa Manzo ba,ba su kawai aka bã su sharĩ'a ba, kuma aka umurce su da binta ba, Banĩ Isrã'ĩla ma an bã su haka kuma sunɗaukaka a kan mutãne a lõkacin da suka yi aiki da sharĩ'ar, kuma suka ƙasƙanta a lõkacin da suka bar aiki da ita. Musulmi ma haka suke idan sun bar sharĩ'ar da Allah Ya aza su a kanta, zã su ƙasƙanta yadda Yahũdawa suka ƙasƙanta.
wannan (Alkur'ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni.
Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi,* Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba?
____________________
  * Ilmin Allah bã shi da iyãka, Yanã bũɗa shi ga wanda Ya ga dãma, a inda kõ a lõkacin da Ya ga dãma, amma dai duk ilmin da bai saukar da shi ga Annabi Muhammadu ba, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, to, bã a aiki da shi ga hukunci kõ sharĩ'a, wanda ya bi shi kuwa, to, ya ɓace ga aikinsa, bã ya cikin shiryayyu mãsu zaman lãfiya a dũniya kuma su shiga Aljanna a Lãhira, dõmin sharaɗin haka shĩne bin sunna. Wanda ya bar sunna kuwa, ya yi kuskuren hanya, bãbu mai shiryar da shi kuma sai Allah idan Yã so shi da rahama, watau Ya sanya shi ya tũba. Wannan ya nũna cewa ibãda da mu'ãmala duka ɗaya suke ga Musulunci, barin aiki da sharĩ'a a cikin kõwannensu duka, kãfirci ne ga wanda ya halatta yin haka nan. Mafi yawan kãfircin da ya sãmi Musulmi, ya zo musu ne ta hanyar barin mu'ãmalõli da sharĩ'ar Allah, suka &# 82auki yin salla da mai kama da ita, shi kaɗai ne Musulunci, suka kãfirta da haka.
Ka ce: "Allah ne ke rãyar* da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
____________________
 * Wãtau ba kũ ne ke rãyuwa da kanku ba, sai an rãyar da ku, haka ne ga mutuwa, bã ku ne ke mutuwa da kanku ba, sai an matar da ku, kuma Allah Shi Ɗaya ke iya rãyarwa ko matarwa. To, yãya ne zã ku ƙi bin sharĩ'ar da Ya umurce ku da binta?.
"Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra."
Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩNã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?"
تقدم القراءة