سورة هود

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Hud a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

To, lalle sũ sunã karkatar* da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.
____________________
  * Bã su son su ga mai yi musu wa'azi, sabõda haka idan sun tsinkãyi Annabi daga nesa, sai su ɓũya, dõmin kada ya gan su, balle ma har ya yi musu wa'azi. Kuma har idan ya sãme su da wa'azinsa, sai su sanya tufãfinsu su rufe idanunsu da kunnuwansu kamar yadda mutãnen Nũhu suka yi masa a lõkacin da yake yi musu wa'azi. Ka dũba sũratu Nũh' sũra ta 71.
Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azãba gare su zuwa ga wani lõkaci ƙidãyayye, haƙĩƙa sunãcẽwa me yake tsare* ta? To, a rãnar da zã ta je musu, ba ta zama abin karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yã wajaba a kansu.
____________________
  * Me ke tsare ta, watau azãbar me ke hana ta ta zo yanzu?. 
Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma Muka zãre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammãnine, mai yawan kãfrci.
Sabõda haka tsammãninka kai mai barin sãshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dõmin sun ce: "Dõmin me ba a saukar masa da wata taska ba, kõ kuma Malã'ika ya zo tãre de shi?*" Kai mai gargaɗi ne kawai. Kuma Allah ne wakili a kan kõme.
____________________
  * Sabõda zaman mutãne bã su girmama mutum sai idan Yanã da wata dũkiya kõ kuma akwai wani ƙarfi bayyananne tãre da shi, to, kai kuma ga zãhiri, bã ka da dukiya kõ wani ƙarfin da zã ka iya tĩlasta su da shi a kan wani abu. Sabõda haka kanã tsõron iyar da duka abin da aka umurce ka, dõmin kada a ƙaryata ka. To, kada ka ji tsõron iyarwã, Allah ne wakili a kan kõme.
Kõ sunã cewa: "Yã ƙirƙira *shi ne."Ka ce: "Sai ku zo da sũrõri gõma misãlinsa ƙirƙirarru, kuma ku kirãyi wanda kuke iyãwa, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya."
____________________
 * Kõ kuwa bã zã ka iyar da abin da aka aike ka ba dõmin tsõron su ce: "Kai ne ka ƙirƙira Alƙur'ãni, sa'an nan ka jinginã shi ga Allah." To, sai ka ce: "Ni mutum ne kamarku, idan nĩ na ƙirƙira Alƙur'ãni, to, bã zai gãgare ku ku ƙirƙira irinsa ba, sai ku zo da surõri gõma irinsa.".
Shin, wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma wata shaida tanã biyar sa daga gare Shi, kuma a gabãninsa akwai littãfin Mũsãabin kõyi da rahama? Waɗannan sunã yin ĩmãni da shi, kuma wanda ya kãfirta da shi daga ƙungiyõyi, to, wutã ce makõmarsa. Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga gare shi. Lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka, amma kuma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.
Ya ce: "Ya mutãnena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Yã bã ni wata Rahama daga wurinSa, Sa'an nan aka rufe ta (ita Rahamar) daga gare ku, shin, zã mu tĩlasta mukuita, alhãli kuwa kũ mãsu ƙi gare ta ne?
Suka ce: "Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa'an nan kã yawaita yi mana jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: "Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to, laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi."
Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini magana a cikin sha'anin waɗanda suka kãfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa ne.
Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili.
"Sa'an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira)."
Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa*, da wanda ya yi ĩmãni." Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan."
____________________
 * Iyalan Nũhu sun yi ĩmãni banda ɗansa Yãmu, da matarsa guda kãfira. Waɗanda suka yi ĩmãni daga sauran mutãnensa tamãnin ne maza da mãtã. Amma kuma an ce mutãne saba'in da biyu ne, kuma an ce gõma ne. Allah ne Mafi sani.
Kuma aka ce: "Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme."Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi*, kuma aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai."
____________________
* Judiyyu sũnan wani dũtse ne a cikin Jazĩra. Jirgin Nũhu ya zauna a kansa, har mutãnen farko na wannan al'umma sun gan shi. Sa'an nan ya halaka.
Aka ce: "Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da waɗansu al'ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa'an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta shafe su daga gare Mu."
"Kuma, ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi, zai saki sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi."
"Bã mu cẽwa, sai dai kurum sashen abũbuwan bautawarmu ya sãme ka da cũtar hauka." Yace: "Lalle ne nĩ, inã shaida waAllah, kuma ku yi shaidar cẽwa" lalle ne nĩ mai barranta ne dagb abin da kuke yin shirki da shi."
Kuma a lõkacin da umurninmu ya je, Muka kuɓutar da Hũdu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõdawata rahama daga gare Mu. Kuma Muka kuɓutr da su daga azãba mai kauri.
Kuma mãtarsa tanã tsaye.* Ta yi dãriya. Sai Muka yi mata bushãra (da haihuwar) Is'hãƙa, kuma a bayan Is'hãƙa, Yãƙũbu.
____________________
  * Matar Ibrãhĩm Sãrah tanã tsaye ga yi musu hidima, sai ta yi dãriyar mamãki, dõmin bãƙin sun ƙi cin abinci. Waɗansu na fassarãwa ta yi haila. Wannan bai dãce ba.
Lalle Ibrãhĩm, haƙĩƙa mai haƙuri ne, mai yawan addu'a, mai tawakkali.
Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: "Yã mutãnẽna! waɗannan, 'yã'yã na* sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku?"
____________________
 * 'Ya'yansa-Yanã nufin mãtan aurensu, dõmin kõwane Annabi uban al'ummarsa ne.Bã ya kamãta a ce wai yanã kiran mazan gari zuwa ga 'ya'yansa uku, dõmin bãbu wata shari'a ta Allah, ga saninmu, wadda ta halattã haɗuwar mazã biyu ko fiye da biyu a kan auren mace guda.
Ya ce: "Dã dai inã da wani ƙarfi game da ku, kõ kuwa inã da gõyon bãya daga wani rukuni* mai ƙarfi?"
____________________
  * Ya faɗi haka dõmin bã shi da dangi a cikinsu. Daga gare shi ba a kuma aiko wani Annabi ba sai a cikin wadãtar danginsa.
Sa'an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre.
Kuma zuwa ga Madyana (Mun aika) ɗan'uwansu* Shu'aibu. Ya ce: "Ya Mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce shi kuma kada ku rage mũdu da sikẽli. Lalle nĩ, inã ganin ku da wadãta**. Kuma lalle inã ji muku tsõron azãbar yini mai kẽwayẽwa."
____________________
* Lãrabãwa ne, sunã zaune a tsakãnin Hijaz da Shãm. ** Inã ganin ku a cikin wadãta; bã ku da bukãtar rage wa mutãne kãyansu. Sabõda haka ku yi adalci ga mutãne wajen ciniki ya fi muku alheri daga dũkiyar haram mai ƙãrewa kõme yawanta.
Ya ce: "Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfaƙãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala."
"Kuma ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare shi. Lalle Ubangijĩna Mai Jin ƙai ne, Mai nũna sõyayya."
Kuma a lõkacin da umurninMu yã je, Muka kuɓutar da Shu'aibu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsãwa ta kama waɗanda suka yi zãlunci. Sai suka wãyi gari guggurfãne a cikin gidãjensu.
Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar* da ake yi musu.
____________________
   * Kyautar la'ana ita ce wadda ake la'antar su da ita a dũniya da Lãhira.
Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe.*
____________________
 * Daga nan zuwa ƙarshen sũra ta'alĩƙi ne dõmin farkarwa. Mai tsayi, watau tana nan tsaye, alãmõminta ba su ɓãce ba, kuma akwai waɗanda suka halaka kamar karan da aka girbe.
Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã* wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto.
____________________
   * Yahũdãwa sun sãɓa wa jũna a cikin littattafan da aka bai wa Mũsã. To, ku Musulmi kada ku bi hanyarsu, har ku sãɓawa Allah, har abin da ya sãme su ya sãme ku.
Sai ka daidaitu* kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
____________________
* Wannan ãyã tanã hana dukan bidi'a a cikin addini. Tun da ba a yarda Annabi ya ƙara ra'ayinsa ba sai dai ya bi umurnin Allah kamar yadda Ya yi umurnin, kuma haka ne Ya umurci wanda ya bi Annabi. Sabõda haka mai sãɓa wa umurnin Allah da ƙãri ko ragi, bã ya cikin mabiyan Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Kada ku karkata* zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba.
____________________
  * Ba ya halatta ga Musulmi ya karkata zuwa ga kãfirai kamar yadda bã ya halatta ya karkata a cikin addininsa. Wannan shĩ ne babban makãmi a kan mãƙĩya.
Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. Wancan* ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.
____________________
 * Tsayar da sallõli farillai tãre da Lĩman a cikin masallatai shĩ ne zikiri ga mai son zikirin gaskiya. Ayyukan ƙwarai sunã shãfe miyãgu.
Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa.(5)
____________________
(5) Haƙuri a kan ibãda wãjibi ne, haka kuma kyautatãwa, wãtau shĩ ne yin kõwãne aiki na ibãda tsantsa kamar salla kõ na ma'amala kamar ciniki da aure, dõmĩn Allah kawai. An yi wa wannan fanni na biyu sũna da "Tasawwuf", bidi'a ne dõmin bai taho daga sunna ba. Asalinsa "theosophy" daga lugar Ajam, ma'anarsa neman hikima ta Allah a hãlin keɓance kai a cikin kaɗaita da wasu aikace-aikace na ibada, kamar girka ga 'yanbõri.
Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alƙaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa.(6)
____________________
   (6) Wannan ãyã da ta sama da ita sunã nũna muhimmancin wa'azi a cikin kõwane hãli na al'umma, dõmin tsarewar zamanta al'umma.
Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan* ne Ya halicce su. Kuma kalmar "Ubangijinka" Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba ɗaya" ta cika.
____________________
 * Allah ya halicci mutãne da hãlãye dabam-dabam dõmin su sãɓa wa jũna.
Verse 122
"Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko* ne."
____________________
 * Ku yi jira ku gani wãne ne zai ci nasara; mũ da muka bi umurnin Allah, kõ kuwa ku da kuke bin zuciyõyinku. Ãƙiba dai tanã ga mãsu taƙawa. Allah ya tabbatar da mu a kan binsa a kan taƙawa. Amin.
تقدم القراءة