سورة لقمان

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Lukuman a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi* dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.
____________________
 * Tatsũniyõyi sunã shagaltarwa daga ilmi mai sanya sanin Allah. Allah Ya hana a yi tarbiyyar yãra game da tãtsũniya mai ɗauke hankalinsu daga ibãda, Littattafan makaranta na zãmani da jarĩdu duka tãtsũniyõyi ne, sai abin da ya dãce da sunna.
Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) "Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take."
"Kuma idan mahaifanka suka tsananta* maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
____________________
  * A bãyan haƙƙin Allah sai haƙƙin iyãye. Sabõda haka ba zã a yi ɗã'a ga iyãye ba ga abin da ya sãɓãwa Allah.
"Kada ka karkatar da kundukukinka* ga mutãne, kada ka yi tafiya a cikin ƙasã kanã mai nũna fãɗin rai. Lalle, Allah bã Ya son dukan mai tãƙama, mai alfahari."
____________________
* Karkata kundukuki ga mutãne, alamar wulãkanta su ne.
"Kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. Lalle mafi mũnin sautuka haƙĩƙa shĩ ne sautin jãkuna.* "
____________________
 * A nan ne iyãkar wasiyyar Luƙmãn ga ɗansa. Sa'an nan kuma Allah Ya ci gaba da bayãnin yadda ake tarbiyyar mutãne.
Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba.* Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
____________________
  * Wannan bayãni ne ga yawan ilmin Allah, watau yanã nũnawa mutãne cewa su yi aiki da ilmin da Ya bã su, mai amfãni zuwa gare su, kada su wuce shi zuwa neman wani ilmi daga wani abu, su bar Allah, su halaka a kan wani ilmi da bai umurce su da su yi aiki da shi ba. Ilmin da Ya bã su a cikin Alƙur'ãni shi ne sharĩ'a wãtau hanya mai kai su ga Aljanna. Sauran hanyõyi ɓata ne.
تقدم القراءة