سورة المجادلة

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Al-Mujadalah a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Lalle Alla Ya ji maganar* wadda ke yi maka jãyayya game da mijinta, tanã kai ƙãra ga Allah, kuma Allah nã jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.
____________________
 * Wannan ƙissa tanã nũna cewa a Majalisar Annabi kõwa na da 'yancin shiga, namiji da mace, kuma ya faɗi abin da yake so, kõ da ya sãɓãwa abin da Annabi ya gani ƙãfin wani wahayi ya sauka. Gã wannan mace sunanta Khaulatu bnt Sa'alabah ta kai ƙãrar mijinta Ausu bn Samit wanda ya yi zihãri game da ita, watau ya ce idan ya kusance ta kamar ya kwãna da uwarsa ne. Ga al'adar lãrabãwa wannan bã saki bã ne, kuma ba ya iya kwana da ita har abada. Wannan shi ne takai ƙarã wurin Annabi har ta yi mahãwar da shi a kansa. Kuma wannan ƙissa tanã nũna gaskiyar Annabi, bai yi jawãbi ba ga abin da bai sãmi wahayi ba a kansa.
Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa* ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ¡iyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme.
____________________
 * A bãyan ƙissar zihãri, ya shiga maganar mãsu gãnãwa a cikin majalisa. Kuma ya nuna cewa ba a sifanta Annabi kõ a jingina wani abu zuwa gare shi sai idan abin nan yã fito daga Allah a cikin harshen ManzonSa.
Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganãwar, sa'an nan sunã kõmã wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma sunã gãnãwa game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai gaishe ka da shi ba, kuma sunã cẽwa a cikin zukatansu: "Don me Allah ba Ya yi mana azãba sabõda abin da muke faɗi?" Jahannama ita ce mai isarsu, zã su shigeta. Sabõda haka makõmarsu ta mũnana.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan an ce muka, *"Ku yalwatã a cikin majalisai," to, ku yalwatã, sai Allah Ya yalwatã muku, kuma idan an ce muku, "Ku tãshi" to, ku tãshi. Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kõme.
____________________
  * Bãyan ƙissar hukuncin gãnãwa cikin majalisa, sai kuma hukuncin zaunãwa kõ tãshi dõmin wani ya zauna. Kuma ana fifita mãsu ilmi da zama ga wurin da ya fi dãcewa da su.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan zã ku gãnãwa da Manzon Allah, to, ku gabãtar da 'yar sadaka* a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
____________________
  * Hukuncin tãyar da mutãne dõmin a gãna da Manzon Allah, bã ya halatta sai a kan larũra mai tsanani sabõda haka aka sanya gabãtar da sadaka, sa'an nan aka sõke shi da umurni da tsaron salla dõmin wa'azin da ke cikinta da kuma bayar da zakka.
Ashe, baka ga waɗanda* suka jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu ba, bã su cikinku, kuma bã su a cikinsu kuma sunã rantsuwa a kan ƙarya, alhãli kuwa sunã sane?
____________________
 * Bãyan maganar mãsu tãyar da mutãne dõmin gãnãwa a cikin majalisa, sai kuma munãfikai mãsu mu'ãmala da kãfirai, kuma su je su zauna cikin majalisar Musulmi dõmin su ɗauki rahõtonsu zuwa ga maƙiyansu.
Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sabõda haka suka kange (mũminai) daga jihãdin ɗaukaka tafarkin Allah. To, sunã da azãba mai wulãkantãwa.
Bã zã ka sãmi mutãne mãsu yin ĩmãni da Allah da RãnarLãhira sunã sõyayya da wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa ba, kõ dã sun kasance ubanninsu ne, kõ ɗiyansu kõ 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yã rubuta ĩmãni a cikin zukãtansu, kuma Yã ƙarfafa su da wani rũhi* daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu babban rabo.
____________________
* Waɗanda suka tsare dõkokin Allah, Allah zai ba su ƙarfin rai ga zartar da al'amuransu da kyau, kuma zai wadãta su a dũniya da Lãhira. Asalin rũhi shine rai. Anã nufin rãyuwar ĩmãni da ƙarfin halin fuskantar gaskiya.
تقدم القراءة