سورة النمل

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar An-Naml a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa* ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani.
____________________
 * Lãhira da ĩmãni da ita sunã a cikin ashĩran Allah. Haka karɓar Alƙur'ãni daga Allah yanã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana a Littafi. Ganin Mũsa ga wutã da abubuwan da suka auku a wurin game da maganar Allah a gare shi da jũyãwar sanda macijiya da kõmawarta sanda da jũyãwar hannunsa fari ƙal da jũyãwarsa zuwa ga asalinsa, duka sunã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana su ga wani mutum.
To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya* ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai."
____________________
 * Abin da ke hakkin ni'imar Allah a kan mutum, ya gõde Masa. Dãwũda da Sulaiman Allah Yã bã su ilmi na Annabci sun tsayu da gõdiyarsa a kan aiki da shi, da kuma iƙrãri da cewa nĩ'ima ce daga Allah, bã da wani aiki nãsu ba. Annabci da ilmi da sanin maganar tsuntsu da ta aljannu da taturũruwa duka sunã cikin ashĩrin Allah da Yake nũnãwa ta hanyar waɗansu bãyinsa Annabãwa.
Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya).
Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai."
Kuma ya binciki* tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?"
____________________
 * Wannan ya nũna tsayuwar sulaimãn da binciken kõme da kõwa a cikin daularsa. Kuma da yadda yake yin tsanani a cikin sauƙi. Wannan ita ce hanyar mulki mai kyau.
"Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne."
"Ga* su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa."
____________________
  * An kãyar da harafin kõrewa dõmin barinsa, da Hausa, yanã ɓãta ma'ana, dõmin shaiɗan bai kange su daga rashin yin sujada ba.
"Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin* Al'arshi, mai girma."
____________________
 * Ya siffanta Allah da cewa bãbu abin bautãwa fãce Shi, dõmin ya kõre cancantar rãnã ga ibãda, da Ubangijin Al'arshi dõmin ya ɗebe girman gadon Bilkisu daga zukãta.
"Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa."
"Kada ku yi girman kai a gare ni, kuma ku zo mini kunã mãsu sallamãwa."
Ta ce: "Yã ku mashawarta*! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta."
____________________
  * Allah bai keɓance hikima ga maza kawai ba har mãtã akwai mãsu hikima a cikinsu. Sai dai Musulunci yã hana shugabancin mãtã, sabõda galibinsu ãdifarsu tã rinjãyi hankalinsu, sabõda kyautata tarbiyyar yãra. Anã fahimtar cewa iya mulki shi ne rashin fallewa da ra'ayi ga shũgaba, sai a bãyan ya shãwarci mutãnensa, kamar yadda sarauniyar Saba' ta yi da Majalisarta.
Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da shi)?"
"Kuma lalle nĩ mai aikãwa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dũbawa ce: Da me manzannin zã su kõmo."
"Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu."
Wanda yake a wurinsa akwai* wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi."
____________________
  * Allah na bãyar da asirai daga littattafai, kõ da wahayi zuwa ga Annabãwa, kõ da ilhãma daga abin da aka bai wa Annabãwa. Waɗansu sun ce ilmin nan sũnan Allah ne Mafi girma. Allah ne Mafi sani. Sai dai sharaɗin aiki da ilmi ga ĩbãda, ya kasance daga Annabãwa kawai, a cikin lõkacin aiwatar da shari'arsu.Bã a iya amfãni da wani sũnan Allah wanda wani Annabi bai zo da shi ba a gabãnin Musulunci, kuma a bãyan Musulunci.
Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye* daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu."
____________________
 * Idan ĩmãni ya shiga a cikin zũciya, sai girman kai ya fita daga gare ta sarauniya Bilkisu tanã kuranye ƙafãfunta da niyyarta ta shiga a cikin ruwa dõmin ta nũna ɗã'arta ga umurnin Annabin Allah Sulaimãn kuma ta yarda da shiga gulbin da ba ta san tsawon zurfinsa ba, kõ da za ta mutu awurin ɗã'ã da taƙawa. Mace da sarauta iyakar girman kai ke nan, bãbu abin da zai gusar da shi sai ĩmãnin gaskiya.
Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?"
Kuma waɗansu jama'a tara* sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa,** shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'."
____________________
  * Yawan mãsu ɓarnã bã ya hana gaskiya bayyana. Kuma mai mãkirci dõmin ya halakar da mai gargaɗin addinin Allah, yanã yi wa kansa sanadin halaka kawai ne. Waɗannan mutãne tara sun yi niyyar kashe Sãlihu ne, bã da sanin danginsa ba, a wurin dayake kwãna yanã salla a masallacinsa, a bãyan gari. A can Allah ya halakar da su. Wannan shĩ ne sakamakon mãkircin da suka ƙulla. ** Zã mu kwãnan masa, ai zãmu kwãna da niyyar kashe shi a cikin dare, a ɓõye.
Ka dũba yadda ãƙibar mãkircinsu ta kasance lalle Mũ Mun darkãke su da mutãnensu, gabã ɗaya.
Waɗancan, gidãjensu ne, wõfintattu sabõda zãluncin da suka yi, lalle ne a wancan akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke sani.
Da Lũdu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Shin kunã jẽ wa alfasha* ne, alhãli, kuwa kunã gani?"
"Shin lalle kũ haƙĩƙa kunã je wa maza da sha'awa baicin mãtã? Ã'a, kũ wasu irin mutãne ne kuna aikin jãhilci."
____________________
  * Alfãshar mutãnen Lũɗu, ita ce luwãɗi, namji yabi namiji a duburarsa wannan alfãsha, kõ dabbõbi bã su yin ta. Ga mutãnen Lũɗuta fãra bayyana. Allah Ya halakar da su kamar yadda Ya ambata. Sa'an nan kuma ba a ƙãra ganinta ba, sai ga wannan al'umma asĩirin da ke ciki, shĩ ne yadda Allah Yake jũyar da ɗabĩ'ar mutum ta zama bã ta mãsu hankali ba, tãre da dõgewar halittar jikinsa kamar yadda take ga zãhiri.
Sai Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa,* fãce mãtarsa, Mun ƙaddara ta a cikin mãsu wanzuwa.
____________________
* Mutãnensa mũminai. Ĩmãni da gaskiya idan gaskiya ta bayyana asĩri ne daga asĩran Allah sai wanda Ya bai wa. Kusanci ga wani Annabi da aure kõ zumunta, bã ya bãyar da shi. Ruwan azãba, shĩ ma asĩri ne na Allah.
Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa. To, ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.
Ka ce: "Godiya ta tabbata ga Alah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa." Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi?*
____________________
 * Daga wannan ãyã ta 59 zuwa ƙarshen Sũra, duka tambĩhi ne ga abũbuwan fake na ilmin Allah, wanda ya shãfi jikunanmu, amma ba mu san yadda suke aukuwa a gare mu ba. Sa'an nan kuma da tambĩhi ga abũbuwan gaibi da suke zuwa dõmin mu yi ĩmãni da su.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne?"
Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci.
Ka ce: "Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta* a gare ku."
____________________
   * Kuturi, shi ne a bãyan wani ya hau dabba ya kuma aza wani a kanta daga bãya gare shi. Kinaya ce na cewa abin yanã kusa gare su ƙwarai, kamar tsakãnin ɗan kuturi da mahayin dabba.
Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa.
Lalle ne wannan Alƙur'ãni* yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.
____________________
  * Idan wannan Alƙur'ani ya ƙunsã ilmin asĩrai da yake iya gaya wa Banĩ Israĩla mafi yawan abin da sũ da kansu, suke sãɓã wa jũna a kansu, tãre da shahararsu da ilmi, da yawan Annabãwan da suka wuce a cikinsu, to, ga Lãrabãwa jãhilai hiyãka ke nan. Bãbu abin da ya wajaba a gare su, sai sallamawa ga abin da yake kiran zuwa gare shi. In abin da yake faɗa ba gaskiya ba ne, dã Banĩ Isrãĩla ne farkon mãsu nũna ƙaryarsa. Ammã ba su yi ba. Sabõda haka duka gaskiya ne. Sai kõwa ya bĩ shi ya tsĩra.
Verse 77
Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai.
Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba* daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni."
____________________
   * Wata dabba ce anã kiranta Jassãsa an ce 'yar rãƙumar Sãlihu ce a lõkacin da aka kashe uwarta, ta gudu, ta shiga cikin dũtse' dũtsen ya rufe da ita. Tanã fitõwa daga dũtsen Safa a Makka da hantsi. Bãyan fitõwarta, bãbu sauran wa'azi. Mũmini ya tabbata mũmini kãfiri kuma ya tabbata haka. Tanã riƙe da sandar Mũsã da Hãtimin Sulaimãn. Tana fitõwa a bãyan fitõwar rãnã daga yamma. Allah ɗai Ya san gaskiyar yadda take.
Kuma da rãnar* da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu.
____________________
  * Bãyan fitõwar dabba, kuma sai bũsar ƙahõ na farkõ, sa'an nan na biyu sa'an nan Ƙiyãma.
Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita,* a yinin nan, amintattu ne.
____________________
  * Firgita daga azãbar Lãhira, wannan firgita ba irin ta farko ba ce wadda aka ambata a cikin ãyã ta 87, dõmin wancan firgitar kwarjini ce a bãyan tãshi daga kaburbura.
(Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari,* Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."
____________________
  * Wannan Gari shĩ ne Makka. Sanya Makka hurumi ba a iya shiga cikinsa da yãki yanã a cikin ashĩrai na Allah. Shiryuwa da ɓata duka asĩrai ne na Allah. Tsãrin Alƙur'ani da abubuwan da ya ƙunsa duka asĩran Allah ne.
Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu." Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.
تقدم القراءة