سورة الحجر

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar A-Hijr a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.*
____________________
  * Kõwane kãfiri yanã gũrin yã zama Musulmi dõmin abin da yake gani na shiriya da ladubban Musulunci, waɗanda ya tabbata bãbu zama lãfiya ga mutum fãce idan yã sãme su, amma shaiɗan yanã hana shi musulunta sabõda waɗansu dalĩlai da yake sanyãwa a ganinsa.
Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."
Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,* bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
____________________
 * Gaskiya a nan anã nufin azãba dõmin zuwanta tabbatacce ne. Dukan abin da yake tabbatacce shĩ ne haƙƙun, watau gaskiya.
Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.
Kamar wancan ne Muke shigar da shi* a cikin zukãtan mãsu laifi.
____________________
   * Shirki da kãfirci da ƙaryatãwa, su duka izgili ne da addini.
Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.
____________________
 * Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanyar mutãnen farko ta ƙaryata Manzanni har a lõkacin da Allah zai halaka su da azãbarsa.
Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.
Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.
Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã* da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.
____________________
  * Muka sanya muku abũbuwan rãyuwa a cikinta, kuma Muka mallaka muku bãyi waɗanda suke bã kũ ne kuke ciyar da su ba, Mũ ne ke ciyar da su game da ku duka. Wãtau aza abũbuwa a kan ma'auni shĩ ne maslaha rashin yarda da tsaron ma'aunin nan shĩ ne izgili.
Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.
Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar* iskar zafi.
____________________
  * Halittar Ãdamu daga yumbu kekasasshe, ya fi daraja bisa halittar Shaiɗan daga harshen wuta, dõmin wuta tanã nũni ga sassabcin hankali da rashin natsuwa.
"To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa* a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."
____________________
 * Wannan ya nũnã Ãdamu an yi halittarsa ne da lãka da Rũhi daga Allah kamar yadda aka halitta Isã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sabõda haka halittar Ãdamu ta fi zama abin mãmãki daga halittar Ĩsã, dõmin Ĩsã asali guda kawai ya rasa daga halittar ɗiyan Adam ta al'ãda, amma halittar Ãdamu tã rasa dukan asalan biyu na uwa da na uba. Haka kuma halittar Hawwã'u, matar Ãdamu tã fi ta Ĩsã ban mãmãki dõmin rashin asalin uwa da ta yi inda ɗã yake ɗaukar lõkacin sũrantãwa, ya fi ban mãmãki daga rashin asalin uba.
Verse 37
Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."
Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."
Verse 43
Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya.
Tanã da ƙõfõfi bakwai,* ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.
____________________
* Ƙõfofin Jahannama bakwai ne, watau ɗabaƙõƙinta ta farko ita ce Jahannama, sa'an nan Lazza, sa'an nan Alhuɗama sa'an nan Assa'ĩra, sa'an nan saƙar, sa'an nan Aljahĩm, sa'an nan Alhãwiya. Kõwace ɗabaƙa tanã da juz'i sananne, watau ƙõfa ga Yahudu, wata ga Nasãra, wata Saba'ãwa, wata ga Majũsãwa, wata ga Mushirikai, wata ga munãfukai, wata ga Musulmi waɗanda aka yi musu hushi (mummunan aiki). Anã fatan fita ga mãsu tauhĩdi daga gare ta. Ba a fatan kõme ga sauran, sunã dawwama a cikinta har abada.
Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.
Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.
Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra* ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"
____________________
  * Ibrahĩm yanã yi musu tambayã ne dõmin yanã ganin kamar sunã yi masa magana ta izgili ne a kan sãmun ɗã a bãyan tsũfansa da na mãtarsa. Sabõda haka suka gaya masa cewa sũ masu gaskiya ne.
Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."
"Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."
"Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."
Verse 64
"Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."
Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.
Verse 69
"Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."
Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna* idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
____________________
* Yanã nufin mãtan garin, dõmin Annabin mutãne shĩ ne ubansu.
Rantsuwa da* rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
____________________
* Allah Yã yi rantsuwã da rãyuwar Annabi Muhammadu, tsĩrã da amincin Allah su tabbata a gare shi. Wannan shĩ ne matuƙar girmamãwar wadda Allah Yake yi wa mutum. Kuma yanã nũna cewa rãyuwar Annabi tanã da muhimmanci ƙwarai.
Verse 73
Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
Verse 76
Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.*
____________________
 * Hanya tabbatacciya ta mutãnen Makka zuwa Syria (Sham).
Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika* sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
____________________
  * Ma'abũta Al'aika, sũ ne mutãnen shu'aibu.
Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.
Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri(5) sun ƙaryata Manzanni.
____________________
 (5) Ma'abũta Hijiri, sũ ne samũdãwa.
Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.
Verse 83
Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu(6) da Alƙur'ãni mai girma.
____________________
 (6) Bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu su ne Fãtiha mai ãyõyi bakwai. Anã karanta su a cikin kõwace raka'a ta salla.
Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
Verse 90
Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,(7)
____________________
  (7) Mãsu rantsuwa a kan sãɓa wa Annabãwa, watau kamar sun yi rantsuwa wa bã zã su bi abin da Annabãwa suka zoda shi ba. Wãtau su ne mãsu tsananin izgili da addini.
Verse 92
To, rantsuwa da Ubangijinka!* Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
____________________
* Allah Ya yi rantsuwa da ZãtinSa a kan Shĩ ne Ubangijin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi, dõmin Ya natsar da ransa daga tsõron mãsu yi masa izgili, kuma dõmin Ya ƙarfafa shi ga zartar da aikin da Ya sanya shi na iyar da Manzanci bã da wata fargaba ba.
Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
Verse 95
Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu* izgili.
____________________
   * Mãsu tsananin izgili ga Annabi waɗanda Allah Ya isar masa daga gare su su biyar ne, daga Bani Asad bn Abdul'uzza bn Kusayyi akwai Aswadu bn el Muttalib, Abu zam'ah, kuma daga Bani Zuhrah akwai el Aswad bn Abdu Yagũth. Daga Bani Makhzumi akwai el walid bn Mugira. Daga Bani Sahmi akwai el Ãs bn wã'il. Daga Banĩ Khuzã'a akwai el Harith bn el-Tulãtilah. Su ne mãsu darajar mutãnensu. A lõkacin da suka dõge da sharri, Allah Ya hũtar da Annabi daga sharrinsu da nau'i-nau'i na masĩfu suka halaka. Dubi ƙarin bayãni daga tafsĩrin bn Kathĩr. tsare Annabi daga gare su, tun yanã shi kaɗaia Makka yã isa ya sanya shi ya dõgara ga Allah bãyan abubuwa sun ƙãra yawa da sauƙi.
Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).
Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
تقدم القراءة