سورة الأحقاف

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Al-Ahkaf a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur'ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa.
Lalle ne waɗanda* suka ce: "Ubangijinmu Allah ne," sa'an nan suka daidaitu, to, bãbu wani tsõro a kansu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba.
____________________
   * Yã fara da wanda ya yi wa kansa nasĩha, kuma ya yi aiki da ita, to, shĩ mai gargaɗi ne. Haka kuma mai yin nasĩha ga mutãne, shĩ mã mai gargaɗi ne.
Kuma Mun yi wasiyya ga mutum* game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in, ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)."
____________________
 * Mutum a cikin iyãlinsa, kõ ya zama mai gargaɗi ga kansa da nasĩha ga mahaifansa da zuriyarsa kamar yadda ya bayyana a cikin ãyõyi 13,l4 da l5, kõ kuma ya zama mai butulci ga kansa, ya tõzartar da iyãyensa da zuriyarsa, kamar yadda ya bayyanaa cikin ãyõyi 17 da 18.
Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah taimako (sunãce masa) "Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne." Sai shi kuma ya ce. "Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."
Kuma ga kõwane nau'i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin (Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su ba.
Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã (a ce musu): "Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi."
Kuma ka ambaci ɗan'uwan* Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi (da cẽwa) "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma."
____________________
 * Ya ambaci hũdu da mutãnensa Ãdãwa da misãlin waɗansu mãsu garagaɗi daga Annabãwan da suka shũɗe da kuma mutãnensu da yadda aka halaka su daga inda suke zaton rahama ta Je musu. Haka ne hukuncin. Dukan wanda aka yi wa gargaɗi da bin umurnin Allah, idan ya ƙi bi, sa'an nan ya bi son zũciyarsa, Allah zai Kãwo masa azãba daga inda yake zaton alheri ga kansa.
Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba, kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya wajaba* a gare su.
____________________
  * Ya wajaba a gare su, watau sakamakonsa ya tabbata a kansu da azãba.
Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo.
Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu* zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi.
____________________
   * Wannan yã nũna cewa a cikin aljannu akwai Musulmi da masu gargaɗi, kuma idan mutum ya yi gargaɗi, dõmin Allah, Allah zai taimake shi da mãsu saurãra masa, kõ da daga waɗansu jinsin da ba nãsa ba. Kuma zama a cikin wani addinin Allah da ya shige, ba ya isa ga wanda bai shiga addinin Musulunci ba, a bãyan bayyanar Musulunci.
Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) "Ashe, wannan bã gaskiya ba ne?" Su ce: "Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!" Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."
تقدم القراءة