سورة الأنفال

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Al'Anfal a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Suna tambayar ka* ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."
____________________
 * Yã fãra Sũrar da tambayar Sahabbai ga Annabi cewa. wãne ne ya fi cancanta da dũkiyar ganĩmar da aka sãmu a yãƙin Badar Babba, samãri mayãƙa kõ tsõfaffi mãsu bãyar da shãwara da ra'ayõyinsu, mãsu kyau. Sa'annan ya yi jawãbi da cewa: "Ka ce ganimar ta Allah ce da ManzonSa," sabõda dalĩlan da suke tafe ga ayõyin da suke biye. Ana nufi wanke sõja daga jãyayya a kan dũkiya. AllahYa fi sani.
Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.*
____________________
 * Watau sunã yin ibãda ta jiki da ta dũkiya wãjiba da nãfila.
Kuma a lõkacin* da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai;
____________________
 * Asalin fitar Musulmi zuwa Badar shi ne Annabi ya ji lãbãrin Abu Sufyãna yã fito daga Makka da ãyari zuwa Shãm, watau "Syria" , sai ya fita dõmin a kãma shi, suka sãmi Abu Sufyãna yã shige da dũkiya, sabõda haka Annabi daga Badar ya kõma Madĩna. Wannan fita, anã kiran ta Badar karama. Da Abu Sufyãna ya sãmi lãbãri, sai ya aika wa Kuraishãwa, dõmin su fito, su tsare dũkiyarsu daga Musulmi. Annabi, da ya ji lãbãrin kõmõwar Abu Sufyãna, sai ya fita tãre da jama'arsa, wanda ya ji Yanã son fita, kuma yanã da abin hawa. Abu Sufyãna tãre da ãyari sũ ne wajen da bãbu ƙaya. Yaƙin Kuraishãwa shĩ ne wajen da yake da ƙaya. Musulmi a tsakiya. Abu Sufyãna ya saki hanya ya tsĩra.Ya nemi Kuraishãwa da su kõma, Abu Jahal ya ce sai Allah Yã yi hukunci a tsakãninsu da Muhammadu wanda ya kãtse zumuntã, ya bar addinin iyãye.
A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa* daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.
____________________
 * A lõkacin zãfi ne na bazara, kuma aka faralta azumi, sai Allah Ya saukar da ruwa daidai da sansanin Musulmi, suka shã, suka yi wanka sa'an nan kuma aka daddale musu rairayi dõmin sauƙin tafiya.
A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu.*
____________________
   * Sa'an nan kuma Annabi da umurnin Allah ya ɗebi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jefa a jihar kãfirai. Bãbu wanda ya rage a cikinsu, fãce tsakuwar nan tã shiga a cikin idãnunsa.
Kuma duka wanda* ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita!
____________________
  * Gudu a wurin yãƙin Jihãdi shĩ ne mafi girman haram duka, matuƙar kãfirai ba su fi ninki biyu na adadin Musulmi ba, kamar yadda zai zo. Wanda ya yi gudu a wurin jihãdi kamar yã nemi kãfirci ya rinjãyi Musulunci ne.
To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa;* kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
____________________
 * Kisan da aka yi musu, Allah ne Ya kashe su, haka Annabi ya ɗebi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jefa wa kãfirai, tsakuwar ta shiga cikin idãnun kõwane ɗaya daga cikinsu. To, wannan jĩfar daga Allah take. Sabõda haka duk ganĩmar dai ta Allah ce da ManzonSa, sai yadda Ya so, zã a raba ta.
Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa, dã sun jũya, alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa.
Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa.
Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijãra mai girma.
Kuma a lõkacin da waɗanda* suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.
____________________
  * Ƙuraishãwa suka tãru sunã shãwarar yadda zã su yi da Muhammadu; kõ su ɗaure shi a cikin gida, kõ su kashe shi, kõ su kõre shi. Ra'ayinsu ya tsaya ga su kashe shi da zãɓaɓɓun mutãne daga kõwace ƙabĩla yadda danginsa, Banĩ Hãshim, bã su iya faɗa da dukkan Lãrabãwa, har su kõma ga diyya. A rãnar da suka shirya kashe shi, Allah Ya umurce shi da hijira zuwa Madĩna. A lõkacin da ya fita daga gidansa ya iske su tsaitsaye, sunã barci, ya zuba turɓãya a kunnuwansu, sa'annan ya shige suka tafi tãre da Abũbakar, suka sauka a cikin kõgon dũtsen Thaur. Bãyan kwãnaki uku, suka fita zuwa Madina.
Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu,* kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri.
____________________
* Rãyuwar Annabi a cikin mutãne aminci ne daga azãba, haka kuma yin istigfãri aminci ne. Wanda ke son wadãta da aminci daga Allah, sai ya lazimci istigfãri da bin sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi* ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.
____________________
* Daga farkon sũrar har zuwa a nan, anã bayãnin cewa ganĩmar Badar bã ta kõwa ba ce fãce Allah da ManzonSa; to, a nan Yanã bayãyin yadda zã a raba dũkiyar, kuma wannan rabon, ya zama sunna ga dukkan dũkiyar ganĩma da Musulmi suka sãmu da yãƙi kõ hari.
A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa'adi, dã kun sãɓa ga wa'adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa. Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani.
A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake a cikin ƙirãza.
Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani al'amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'umurra.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci* Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.
____________________
* Ambaton Allah bayyane yã fi kyau a wurin yãƙi da wurin harama da hajji kõ umra, kuma da lõkacin da ake fitã zuwa ga masallacin ĩdi. Wurin da bã waɗannan wurãre uku ba, ambaton Allah, ya zama asirce yã fi kyau.
Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu,* sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.
____________________
 * Kada Musulmi su fita zuwa yãƙi da nũna alfahari da kiɗe-kiɗe da giya da mãtã da maganganun alfãsha, kamar yadda Kuraishãwa suka fita zuwa Badar; ku fita da tawãlu'i da zikirin Allah.
Kuma a lõkacin da Shaiɗan* ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne."
____________________
* Shaiɗan ya fita zuwa ga Ƙuraishãwa a cikin sũrar surãƙ atu bn Mãlik, ya ce musu Yanã tãre da su, kuma shi ne maƙwabcinsu; watau danginsa, Kan'ãnãwa, bã zã su taɓã su ba da yãƙi, a lõkacin da suke yãƙi da Muhammadu. Bãyan haka da ya tafi Badar yã ga Malã'iku, shĩ ne ya kõma bãya, yanã c ewa wai shi yanã tsõron Allah; watau yanã yi wa Ƙuraishãwa izgili; sũ ne bã su tsõron Allah.
Kuma dã kã gani, a lõkacin da Malã'iku suke karɓar rãyukan waɗanda suka kãfirta, sunã dukar fuskõkinsu da ɗuwãwunsu, kuma suna cẽwa: "Ku ɗanɗani azãbar Gõbara."
To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre* waɗanda suke a bãyansu, game da su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa.
____________________
   * Wãtau a kashe waɗanda aka kãma dõmin saura su gani su ji tsõro.
Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi,* kuma da ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba a zãluntar ku.
____________________
* Tattali daga wani ƙarfi, ya haɗa dukkan abin da zai yiwu a yi yãƙin abõkin gãba da shi. A yanzu daga bindiga da abin da yake sama da ita, shi ne zã a yi tattali.
Bã ya kasancewa* ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
____________________
* Bayan da Musulmi suka ci nasara a Badar, suka kama Kuraishãwa a cikinsu har da Abbas baffan Annabi. Sai Annabi ya shãwarci Sahabbansa ga abin da zã su yi da kãmammu. Abubakar ya ce wa Annabi, "Mutãnenka ne, ka sake su." Sa'an nan ya nemi Umar shãwara, ya ce masa: "Ka kashe su." Sai ya karɓi fansa daga gare su. Bãyan haka Alƙur'ãni ya sauka da ƙarfafa ra'ayin Umar na a kashe su, ya fi. Amma tun da an riga an zartar da fansar, shĩ ke nan.
Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta,* dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma.
____________________
* Abin da ya gabãta na Littãfi shi ne, amma Allah ne Masanin haƙĩƙa, abin da yake a cikin sũrar Ãl Imrãna, ãyã ta l59, inda aka bai wa Annabi umurnin ya yi shãwara da Sahabbansa ga abin da ya shãfi yãƙi, sa'an nan kuma ya dõgara ga Allah wajen zartar da abin da ya zãɓã daga shãwarar da suka bã shi.
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira* ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.
____________________
* A farkon Musulunci hijira sharaɗi ce ga shiga cikin waliccin Musulmi, amma bãyan da Musulunci ya yi ƙarfi, hijira ba ta zama sharaɗi ba, sai dai tanã wajaba ga Musulmi ya tashi daga inda bã ya iya tsare addininsa zuwa ga inda yake iya tsare shi, matuƙar bãbu wata wahala mai tsanani. Ana taimakon Musulmin da bai yi hijira ba ga abin da bai shãfi warware alkawarin Musulmi ba.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abũta zumunta, sãshensu ne waliyyan* sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani.
____________________
 * Walicci shi ne kusanta da lizimtar wajabcin taimakon jũna.A farkon Musulunci, Musulmi bã su da walicci a kan wani Musulmi, sai idan yã yi hijira zuwa Madĩna. Bãyan cin Makka da wãtsuwar Musulunci sai waliccin Musulmi ya wajaba a kan kõwane Musulmi a inda duk yake, a cikin dũniya, gwargwadon hãli, amma kuma a cikin haka mafi kusantar zumuntã shi ne mafi cancanta da waliccin kõwane Musulmi, har dai ga abin da ya shãfi hãlãye na zaman mutum kamar aure da gãdo, da sauransu, kamar yadda littattafan sunna suka bayyana, a can cikin bãbin walicci.
تقدم القراءة