سورة النحل

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar An-Nahl a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi* daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
____________________
  * Saukar da malãiku da Rũhi watau Alƙur'ãni a zãmanin Annabci kõ kuma fahimta da ƙarfin zũciya waɗanda Allah ke sanyãwa ga wanda Ya nufa da jaddada addĩni a kan kõwane ƙarni. Aiko mãsu gargaɗi shĩ ne mafi girman ni'imar Allah a kan mutãne.
Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci.
Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã.
Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai.
Kuma da dawãki* da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba.
____________________
  * Haɗa dawãki da alfadarai zuwa ga jãkuna kuma aka ce dõmin "hawansu da yin ƙawã" yana nũna cewa ba a cin dawãki da alfadarai dõmin an san cewa an hana cin jãkuna a lõkacin yãƙin Khaibara, kuma ãyõyin da ke gaba da wannan ãya sun nũna anã cin dabbõbin ni'ima kuma anã hawansu, kuma cin nãma yã fi hawa zama ni'ima, sabõda haka, shĩ ne ya kamãta a ambata inda ya halatta. Wannan ne mazhabar Mãliki da Ahu Hanĩfa, kuma shĩ ne maganar Abdullah bn Abbãs Allah Ya yarda da su. Wasu sun ce ana cin dawãki da alfadarai dõmin cewa, "Anã hawansu dõmin ƙawa," bã ya hana a yi wani abu da su, wato cin nãmansu, dõmin a cikin Bukhãri daMuslim an ruwaito halaccin cin dawãki. Wannan shĩ ne maganar Al-Hasan da Shuraih da 'Aɗa' a da Sa'ĩd bn Jubair. Kuma Shi ne mazhabar shãfi'i da Is'hãƙ. Sun yi hujja da halaccin nãman dawãki da abin da Asmã'u bint Abĩ Bakar Assiddiƙ ta ce, "Mun sõke wata gõɗiya' muka ci a zamanin Manzon Allah,a Madina." Kuma a cikin Bukhãri da Muslim daga jãbir, Allah Ya yarda da shi, "Mun ci dawãki da jãkunan jeji a Khaibara, kuma Annabi tsira da aminci sun tabbata a gare shi, ya hana jãkunan gida" Acikin Abĩ Dãwud, "Mun yanke dawãki da alfadarai da jakuna alhãli yunwa ta kãmã mu, amma sai Annabi ya hana mu cin jãkuna da alfadarai, bai hana mu cin dawãki ba" Nĩ, a ganina, ra'ayin cin dawãki ya fi ƙarfi dõmin sũrar ta sauka a Makka, amma hadisin yankan gõɗiyar, a Madĩna aka yi shi. Saboda haka surar ba ta shãfe shi ba. Dũbi Radd Al-Azhãn.
Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa.
Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci).
Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa,* sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba.
____________________
 * Kamar yadda Allah Ya halaka Bukht Nasar. Aka halaka shi da ginin gidansa. Allah Yanã halaka kãfirai da abin da suke tãnadã wa kansu dõmin nħman rãyuwarsu.
Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗanda suka kãfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã.
Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni.
Kuma sunã sanya rabõ *ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa.
____________________
 * Sunã sanyãwar rabõ daga dabbõbi da hatsi ga gumãka kõ aljannu, alhãli ba su san amfãnin da gumãkan kõ aljannun suke iya jãwo musu ba kõ suke tunkuɗewa daga gare su. Akwai daga cikin ni'imõmin Allah, Ya shiryar da mutãne ga gãne cewa waɗannan gumãka da aljannu kõ wani mahalũƙi bã ya iya cũta kõ jãwo wani amfãni fãce da iznin Allah. Sabõda haka bãbu wanda ya cancanci a bauta masa fãce Allah, Mai tumɓuke cũta kuma Mai jãwo amfãni. Watau wannan bãyar da ni'imar 'yancin ɗan Adam kãmilan, su duka bãyi ne, bãbu daraja ga kõwa sai da taƙawa.Sanin haka wata ni'ima ce daga Allah.
Kuma sunã danganta 'ya'ya mãta ga Allah. Tsarkinsa yã tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha'awa.
Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace* sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki.
____________________
  * Fahintar cewa ɗã namiji da'ya mace duka ɗaya suke, da hana kashe su kõ turbuɗe su, wata ni'ima ce babba da 'yancin mãtã babba, a cikin rãyuwar ɗan Ãdam.
Ga waɗanda ba su yi ĩmãni* da Lãhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.
____________________
 * Ƙãrin bãyani ne ga abin da ya gabãta kuma na bãya da shi ya rãtayu da shi, shiryarwa zuwa ga halãye maɗaukaka ni'ima ce babba.
Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu,* dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta ba.
____________________
  * Rashin halaka dũniya sabõda laifin mutãne da rashin kãmasu da dukan laifinsu, ni'ima ce babba.
Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye* da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.
____________________
* Yã ambaci abin mãye a cikin abũbuwan ni'ima a gabãnin aharamta giya. Kuma haramtã ta bã ya hanã ta zuma a cikin ni'imõmin Allah ga mutãne dõmin an haramtã ne sabõda tsaron hankalinmu a kan neman waɗansu ni'imõmin da suka fĩ ta a Aljanna a inda bã zã a hana ta ba sabõda ƙarewar taklĩfi a can. Sabõda haka ne ya ƙãre ãyar da cewa: "Akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.".
Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi* zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa."
____________________
  * Wahayi na ilhama, watau Allah Ya cũsa wa ƙudan zama ilmin yin sã ƙar gidan zuma da gãne hanyõyin tafiya ta kõma gidanta, da cin kõwane irin furen itãce dõmin a fitar dani'imar abin sha mai dãdi ga mutãne, kuma wanda ya ƙunsa dukkan mãgani ga ciwarwatansu. Wannan ni'ima ce babba.
Kuma Allah Ya fifita sãshenku* a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu?
____________________
  * Arziki daga Allah yake, yanã fĩfĩta waɗansu bãyinsa da arziki a kan waɗansu, sa'an nan wanda aka bai wa arziki daga ckinsu bã ya iya mayar da arzikin a tsakãninsa da wani bãwa nasa har su zama daidai a kan arzikin. to, idan haka ne, yaya kuke sanya waɗansu bãyin Allah daidai da Allah wajen bautarku gare su?.
Kuma ga Allah gaibin* sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne.
____________________
  * Ɓõye lõkacin Ƙiyãma a bãyan bayãnin tabbatar aukuwarta yanã daga cikin ni'imõmin Allah, dõmin mai hankali ya yi tattãli sabõda ita.
Shin ba su ga tsuntsãye* ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
____________________
* Tsuntsãye hõrarru a cikin sararin sama, ana nufi da su, a ganĩna, Allah ne Ya san haƙĩƙa, su ne jirãgen sama, sabõda ambaton hõrewa tãre da sũ a cikin sararin samãniya, dõmin abin da aka hõre, ana hõronsa ne dõmin a ci amfãninsa a lõkaci da wurin hõron. Tsuntsãyen al'ãda bã su da wani amfãni a gare mu a lõkacin da suke a cikin sãrãrin sama. Sabõda haka bãbu wani abu, sai jirgin sama. Bã zã a ce anã nufin shãho ba a lõkacin farauta, dõmin wannan amfãni yã yi kaɗan bisa ga abin da sũrar take ƙidãyãwa na ni'imõmin Allah a kan mutãne gabã ɗaya. Farauta keɓãɓɓiya ce ga mutãnen ƙauye kawai.
Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu* da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci.
____________________
   * Sũfi, shi ne gãshin tumãki mai kama da audugã, wabar shi ne gãshin rãƙumi mai laushi, sha'ar, shi ne gãshin awaki da gezar dawãki. Bai ambaci audugã da kattãni ba, dõmin a wajen shũka suke.
Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna *sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa.
____________________
  * Rĩgã dõmin zãfi da sanyi daga sũfi da wabar da gãshi da audugã da kattãni da rĩga dõmin makãmi shi ne sulke, dõmin makãmi daga baƙin ƙarfe yake kamar takõbi, mãshi da kibiya.
To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã.
Kuma ku cika da alkãwarin* Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa.
____________________
* Wanda yake rantsuwar alkawari da wani, sa'an nan ya warware rantsuwar dõmin neman ya ƙulla wata rantsuwa da wani mutum sabõda wani amfãninsa kõ jama'arsa a cikin wata kabĩla wadda ta fi ta mutãnen farko ƙarfi to, siffarsa kamar mace ce mahaukaciya, mai yin zare, a bayan ta tukka shi, ya yi ƙarfi, sa'an nan ta warware shi. Sabõda haka idan ta so mayar da shi wani zare, to, bã zai yi kyau ba kamar zaren farko da ta yi kuma mutãne sun gãne haukarta, bã zã su yi wata ma'ãmala da ita ba. Wanda ya yi rantsuwa da Allah a kan abu, to, yã sanya Allah lãmuni ke nan. Bã ya halatta ga wanda ya shugabantar da Allah ga wani abu, sa'an nan ya kõma bãya ya ƙi cika wannan alkawarin dõmin bai kiyãye girman Allah ba, wanda ya sanya a tsakaninsa da abõkin ma'ãmalarsa. Tsaron alkawari ni'ima ne.
Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma.*
____________________
   * Wanda yake yin rantsuwa da Allah dõmin ya yaudari wani, to, yanã rũsa kansa ne da kansa, kuma Allah Yanã ħbe jãrumci da natsuwa daga zũciyarsa, sa'an nan kuma yanã da wata azãba mai girma a Lãhira idan Allah bai gãfarta masa ba, da tũba kõ da wani sababi. Sanin haka ni'ima ne.
Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Sa'an nan idan ka karantã *Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe.
____________________
  * An yi saɓãni ga zaman Isti'ãza gabãnin karãtu kõ a bãyansa. Mãlik ya zãɓi a yi 'Isti'ãza' bãyan karãtu, kõ a bãyan an ƙãre yin salla, dõmin kada shaiɗan ya rinjãyi mutum a bãyan ĩmãninsa da salla. Sabõda haka ya karhanta shi a cikin salla. Wasu kuma sunã isti'ãzã a gabãnin karãtu kõ a gabãnin salla.
Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne.
Ka ce: "Rũhul ¡udusi* ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma (dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi."
____________________
 * Rũhul Ƙudusi, watau rai mai tsarki, anã nufin Jibrilu, amincin Allah ya tabbata a gare shi.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin (cẽwa) lalle ne sũ, sunã cẽwa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ãni) harshe ne Balãrabe bayyananne.
Kuma Allah Ya buga misãli,* wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.
____________________
 * Kamar Makka. Annabi Muhammadu ya je musu sun ƙaryata shi, sai Allah Yã musanya amincinsu da tsõro, kuma wadãtarsu da yunwa. Wannan shĩ ne sakamakon ridda a kõwane lõkaci.
Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.
Sa'an nan ku ci daga* abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa.
____________________
* Bãyan bayãni a kan hukuncin ridda sabõda sanyãwar sãshen ni'imõmin Allah ga wasu gumãka kõ aljannu kõ waɗansu mutãne sãlihai, sa'an nan Ya yi umurni da cin abin da Allah Ya azurta mutum duka amma da sharuɗɗa uku, watau ya zama halas ga shari'a kuma mai dãɗin ci, wani haƙƙi na wani mutum bai rãtaya ba a kansa ga shari'a, kuma a bi shari'a wajen aikatar da shi kamar yadda Allah Ya ce wajen yanka da mai kama da shi, shi ne gõde wa Allah. Sabõda haka banda kamar giya da kãyan wani mutum sai fa a bisa yardarsa.
Abin sani kawai (Allah) Ya haramta* muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
____________________
  * Bayãnin abũbuwan da aka haramta, idan bãbu larũra. Anã cin abin da shari'a ta hana a ci a kan larũra sai idan larũrar ta sãmi mutum ne a cikin hãlin sãɓon Allah, kamar mai fita daga ɗã'ar sarkin Musulunci ya yi tãsa ƙungiya dabam, kõ wanda ya fita dõmin wani zãlunci kamar sãta ga misãli, to, ba su cin haram dõmin su ci gaba da aikinsu.
Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni,* kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
____________________
 * Gabãnin wancan sũra, kamar a cikin sũratul An'ãm ãyã ta l46. Sabõda haka bã a biyar da Yahũdu a wajen haramcin abin da Allah Ya haramta musu, su kaɗai sabõda zãluncinsu.
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki* da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
____________________
   * Wanda ya yi wani abu da Allah Ya hana wajen ni'imõmi ko wajen wani abu dabam na sãɓon Allah, to, idan ya tũbã A gabãnin ya kai ga gargara, Allah zai gãfartã masa. Wannan ni'ima ce.
Lalle ne Ibrãhĩm* ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
____________________
   * Akwai daga ni'imõmin Allah,Ya sanya mutum maɗaukaki sabõda addininsa da ĩmãninsa ga Ubangijinsa, kuma Yã bã shi ĩkon binsa da taƙawa kamar yadda Ya yi wa Ibrahĩm. Kuma akwai daga ni'imõmin Allah Ya sanya mutum a cikin zuriyyar mutumin kirki kamar yadda Ya yi wa Annabi Muhammadu Ya sanya shi a cikin zuriyyar Ibrãhĩm.
Mai gõdiya* ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.
____________________
 * An ambaci Ibrãhĩm sabõda ya gõde wa ni'imõnin Allah dõmin Musulmi su yi kõyi da shi wajen gõde wa Allah ga ni'imõmin da Ya yi ishãra zuwa gare su a cikin wannan Sũra da watanta. Gõde wa ni'ima wata ni'ima ce.
Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), "Ka* bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.'
____________________
 * Yanã cikin ni'ima ga Ibrãhĩm da kammalarta a gare shi a umurci mafĩfĩcin tãlikai Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, da bin aƙĩdar Ibrãhĩm.
Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa.(5) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã.
____________________
  (5) Waɗanda suka sãɓa wa jũna a cikin sha'anin Ibrahĩm wanda yake ya kasance yanã girmama Juma'a dõmin ita ce rãnar cikon ni'imõmin Allah a kan bãyinsa. Yahudu suka sãɓã wa Ibrãhĩm suka girmama Asabar dõmin a rãnar nan ne bãbu wani aiki. Wannan ya dõge har a bãyan ɗauke Ĩsa. Nasãra suka jũya dõmin ƙin Yahũdu zuwa ga Lahadi, dõmin su yi daidai da Kaisara, Ƙustantin, mai girmama Lahadi, rãnar bautã wa rãnã. Kafirce wa ni'ima azaba ce.
Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima(6) da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
____________________
 (6) Kira zuwa ga hanyar Ubangiji, Allah, yanã daga cikin abũbuwan kõyo daga Ibrãhĩm kuma kira zuwa ga Allah na daga cikin ni'imõmin Allah ga mai kiran da wanda ake kiran sa'an nan zaman kiran da hikima da wa'azi mai kyau, ni'ima ce ga mai yi da waɗanda ake kira zuwa ga shiriyar duka. Abin da ake cħwa Hikima shĩ ne a yi magana a kan hujja wadda abõkin husũma bã zai iya kauce mata ba.
Kuma idan kuka sãka(7) wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri.
____________________
 (7) Kuma mai kiran mutãne zuwa ga Allah lalle ne sai ya haɗu da cũtarwa daga mutãnen da bã su son gaskiyã. To, Allah bã Ya son zãlunci ko dã a kan maƙiyansa, sabõda haka Ya yi umurni da yin ƙisãsi da misãlin uƙũba, kõ a yi haƙuri, amma yin haƙuri yã fi rãmãwa dõmin nħman ni'imar Allah ta ƙãra kammala.
تقدم القراءة