سورة الفرقان

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Al-Furkan a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana.
Ã'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a.
Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can.
To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma.
A rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã cẽwa,"Allah Ya kiyãshe* mu!"
____________________
 * Asalin maganar shĩ ne "Tsari tsararre," wãtau muna neman tsari daga Allah, tsari tabbatacce.
Ma'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla.
Kuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da malã'iku, saukarwa.
Sai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yinMu." sai Muka darkãke su, darkãkewa.
Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida* suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.
____________________
  * Dabbõbin gida sun fi rashin hankali bisa ga na dãji, dõmin na dãji na gudun abin da zai cũce sũ su kuma dabbõbin gida sunã zamã tãre da mãsu cin su, su shã nõnonsu kuma su kashe 'ya'yansu.
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa* shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci.
____________________
 * Sarrafa Alƙur'ãni watau Munsanya shi a cikin misãlai dabam-dabam dõmin su gani kõ su ji, su yi tunãni, amma sai suka ƙi saurãren, sai dai kãfirci.
Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi* a ciƙin kõwace alƙarya.
____________________
  * Dã Muna so dã Mun aika wa kõwane gari da Annabinsa mai yi musu gargaɗi, amma ba Mu so haka ba, sai Muka aika ka kai ɗaya zuwa ga dukan dũniya dõmin Mu ɗaukaka darajarka.
Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya* zuwa ga Ubangijinsa."
____________________
 * Bã na neman wata ijãra sabõda inã karanta muku Alƙur'ãni, ko, sabõda inã shiryar da ku, amma wanda ya so ya ciyar da dũkiyarsa dõmin Allah, to, shĩ kam bã ni hana shi, sai ya ciyar. Kuma mun sani Annabi ba ya cin sadaka. A kan haka ne waɗansu Malamai suka hana karɓar ijãraa kan karantar da Alƙur'ãni. Abin da yake Mu'utamadi ya halatta sabõda Hadĩsi, kumada sauƙaƙewa ga aikin yãɗa addĩnin Musulunci. Hukumci yanã canzawa da canzãwar hãli.
Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da* Shi.
____________________
 * Idan kanã son sanin siffofin Allah, sai ka tambayi Allah, dõmin bãbu wanda ya san shi, sani na gani balle ya iya gaya maka yadda Yake, sabõda haka siffõfin Allah da sũnãyenSa duka bã a yin shisshigi a gare su, sai yadda aka ji su daga Manzon Allah.Tauƙifiyyai ne.
Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana* ta ƙãra musu gudu.
____________________
* Kõ sun san gaskiyar abin daaka kira su zuwa gare shi, bã zã su yi ɗã'ã ba, dõmin wai sunã jin nauyi su karɓi umurni daga wani mutum.
Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai* (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta.
____________________
* Taurãri bakwai waɗandaake cewa matafa su ne Mirrikh da Zahra da Uɗãrid da Ƙamar, wãtau Watã, da Rãnã, da Mushtari, da Zuhal; Kuma burjõji sũ gõma sha biyu ne, su ne Himlu, da Saur, da jauzã'a, da Sirtãn, da Asad, da Sunbula da Mĩzãn da Aƙrab, da Ƙausu, da Jadyu,da Dalwu da Hũt.
Kuma bãyin Mai rahama(5) su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya).
____________________
   (5) Bãyan da ya ambaci masu ƙin su yi sujada ga Mai rahama sabõda kangararsu sai kumaya fãra ambaton siffofin mãsu son yin sujada gare shi, Yãyi musu sunã Bãyin Mai rahama.
Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu.
Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra(6)
____________________
  (6) Garama, ita ce uƙũba da dũkiya mai lazimtar wanda aka aza wa ita. Da Hausa anã cewa tãra. Watau azãba da zã tafi ƙarfin jiki har tanã neman wani abu wanda ya danganci jiki. Kõ mene ne, kamar dũkiya.
Verse 66
"Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni."
Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa.
Kuma wanda ya tũba,* kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah.
____________________
* Wanda ya tũba daga kõwane irin zunubi, waɗanda aka ambata da waɗanda ba a ambata ba, kõ dã laifinsa kãfirci ne, to, sai ya tũba zuwa ga Allah kawai, tũba ta gaskiya, lalle ne Allah zai karɓi tũbarsa matuƙar ajalin mutuwa bai sauka a kansa ba.
Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci.
Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame* da makãfi.
____________________
 * Idan an yi musu wa'azi zã su saurãre shi, kuma su yi aiki da shi. Bã zã su zama kurãme ba ga karɓar gaskiya, kuma bã zã su zama makãfi ba gaganin hanyar shiryawa.
Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya* mu shũgabanni ga mãsu taƙawa."
____________________
 * Anã son mutum ya rõƙi Allah Ya ɗaukaka shi, shi da zuriyarsa, ɗaukakar addini, kamar yadda Annabi Ibrãhĩm ya yi rõƙon haka. Kuma wannan yanã cikin sifõfin Bãyin Mai rahama.
Ka ce: "Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku* ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci."
____________________
 * Wannan yanã nũna cewa Allah Yanã son bãyinSa mãsu rõƙonsa. Kuma Yanã son a rõkeShi ƙwarai.
تقدم القراءة