سورة الحشر

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Al-Hashr a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Shĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi,* daga gidãjẽnsu da kõra** ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri.
____________________
  * Mazõwa Littãfi a nan, sũ ne Yahũdun Madĩna, watau Banĩ Nadĩr. ** Kõrewa daga ƙasã, Annabi yã kõre su zuwa Haibara a gargaɗar farko, Umar ya kõre su daga Haibara zuwa Syria a gargaɗa ta biyu.
Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya* (matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne.
____________________
 * Ɗan hanya, shĩ ne matafiyin da guzuri ya ƙãre masa, yanã neman taimakon da zai mayar da shi garinsa.
Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu,* sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
____________________
 * Muhãjirĩna sun yi hijira zuwa Madĩna daga Makka kõ waɗansu wurãre. Ansar, su ne mutãnen Madĩna. Waɗannan sũ ne ya kamãta a yi mãmãkin yadda suka taimaki addini a lõkacin tsanani. Muhãjirina sun bar gidãjensu da dũyarsu sun yi hijira, Ansarai sun raba dũkiyarsu da gidãjensu da iyãlansu sun bai wa Muhãjirĩna dõmin taimakon addĩni.
Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci*ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, "Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan?" Alhãli kuwa Allah na shaidar cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne.
____________________
 * Bãyan ya nũna yadda Allah ke taimakon mai binsa da taƙawa. Kuma yanã nũna yadda Yake tãɓar da mai binSa da munãfinci.
Lalle idan an fitar da su, bã zã su fita tãre da su ba kuma lalle idan an yãƙe su bã zã su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙĩƙatan, zã su jũyar da bãyansu dõmin gudu, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba.
Kamar misãlin waɗanda* ke a gabãninsu, bã da daɗẽwa ba, sun ɗanɗani kũɗar al'amarinsu, kuma sunã da wata azãba mai raRaɗi.
____________________
* Kuraishãwa da aka kashe a Badar.
Sai ãƙibarsu ta kasance cẽwa su biyun duka sunã a cikin wutã, sunã mãsu dawwama a cikinta. "Kuma wannan shĩ ne sakamakon mãsu zãlunci."
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa.*
____________________
   * Daga wannan ãyã ta l8 zuwa ƙarshen sũra, yanã bayãnin hãsalin darasin sũrar ne dunƙule, da kuma ambatar muhimman abũbuwan da ta ƙunsa dõmin wa'azi da farkarwa ga mai hankali.
تقدم القراءة