سورة الليل

الترجمة الهوساوية

Fassarar Surar Al-Lail a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Verse 1
Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
Verse 6
Kuma ya gaskata kalma* mai kyãwo.
____________________
 * Kalma mai kyãwo ita ce Kalmar shahãda da abin da ta ƙunsa na addinin Musulunci, wanda yake yinsa kamar yadda Allah Ya ce, ta hanyan ManzonSa, shi ne taƙawa.
Verse 7
To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
Verse 9
Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
Verse 10
To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
Verse 14
Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
Verse 17
Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta.
____________________
 * Mafi taƙawa da Mafi shaƙãwa suna ma'anar mai taƙawa da shaƙiyyi.
Verse 21
To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).
تقدم القراءة