Fassarar Surar Al-Kamar a الهوساوية daga الترجمة الهوساوية
Verse 1
ﮬﮭﮮﮯ
ﮰ
Sã'a ta yi kusa, kuma wata (7)ya tsãge.
____________________
(7) Ƙuraishãwa suka nemi Annabi ya yi addu'a dõmin wata ya tsãge wani ɓangaren nãsa ya fãɗo a ƙasã; ya yi addu'ar, watã ya tsãge, wani abu daga gare shi ya fãɗo kamar yadda suka nema.
____________________
(7) Ƙuraishãwa suka nemi Annabi ya yi addu'a dõmin wata ya tsãge wani ɓangaren nãsa ya fãɗo a ƙasã; ya yi addu'ar, watã ya tsãge, wani abu daga gare shi ya fãɗo kamar yadda suka nema.
Verse 2
Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
Verse 3
Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
Verse 4
Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
Verse 5
ﯪﯫﯬﯭﯮﯯ
ﯰ
Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
Verse 6
Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.
Verse 7
¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.
Verse 8
Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"
Verse 9
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.
Verse 10
ﭯﭰﭱﭲﭳ
ﭴ
Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."
Verse 11
ﭵﭶﭷﭸﭹ
ﭺ
Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
Verse 12
Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.
Verse 13
ﮅﮆﮇﮈﮉ
ﮊ
Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.
Verse 14
ﮋﮌﮍﮎﮏﮐ
ﮑ
Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
Verse 15
ﮒﮓﮔﮕﮖﮗ
ﮘ
Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
Verse 16
ﮙﮚﮛﮜ
ﮝ
To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?
Verse 17
Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Verse 18
ﮦﮧﮨﮩﮪﮫ
ﮬ
Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?
Verse 19
Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.
Verse 20
ﯘﯙﯚﯛﯜﯝ
ﯞ
Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
Verse 21
ﯟﯠﯡﯢ
ﯣ
To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?
Verse 22
Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Verse 23
ﯬﯭﯮ
ﯯ
Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
Verse 24
Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.
Verse 25
"Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"
Verse 26
ﰅﰆﰇﰈﰉ
ﰊ
Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
Verse 27
Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar* ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
____________________
* Mutãnen Sãleh sun nemi mu'ujiza da rãƙuma, a fitar da ita daga dũtse, sai aka fitar da ita, kuma aka raba ruwan sha a tsakãninsu da ita.
____________________
* Mutãnen Sãleh sun nemi mu'ujiza da rãƙuma, a fitar da ita daga dũtse, sai aka fitar da ita, kuma aka raba ruwan sha a tsakãninsu da ita.
Verse 28
Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.
Verse 29
ﭛﭜﭝﭞ
ﭟ
Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,
Verse 30
ﭠﭡﭢﭣ
ﭤ
To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?
Verse 31
Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
Verse 32
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Verse 33
ﭶﭷﭸﭹ
ﭺ
Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
Verse 34
Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.
Verse 35
Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.
Verse 36
ﮏﮐﮑﮒﮓ
ﮔ
Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.
Verse 37
Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa."
Verse 38
ﮟﮠﮡﮢﮣ
ﮤ
Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.
Verse 39
ﮥﮦﮧ
ﮨ
To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.
Verse 40
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Verse 41
ﮱﯓﯔﯕﯖ
ﯗ
Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.
Verse 42
Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.
Verse 43
Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?
Verse 44
ﯫﯬﯭﯮﯯ
ﯰ
Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"
Verse 45
ﯱﯲﯳﯴ
ﯵ
Zã a karya* tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
____________________
* Bushãra ce ga Annabi, cewa zai yi yãƙi da Kuraishi kuma zai rinjãye su. Sa'an nan yãkin ya auku a Badar.
____________________
* Bushãra ce ga Annabi, cewa zai yi yãƙi da Kuraishi kuma zai rinjãye su. Sa'an nan yãkin ya auku a Badar.
Verse 46
ﯶﯷﯸﯹﯺﯻ
ﯼ
Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.
Verse 47
ﯽﯾﯿﰀﰁ
ﰂ
Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
Verse 48
Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."
Verse 49
ﰍﰎﰏﰐﰑ
ﰒ
Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
Verse 50
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖ
ﭗ
Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
Verse 51
ﭘﭙﭚﭛﭜﭝ
ﭞ
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
Verse 52
ﭟﭠﭡﭢﭣ
ﭤ
Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
Verse 53
ﭥﭦﭧﭨ
ﭩ
Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
Verse 54
ﭪﭫﭬﭭﭮ
ﭯ
Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
Verse 55
ﭰﭱﭲﭳﭴﭵ
ﭶ
A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
تقدم القراءة