ترجمة سورة الصافات

Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
ترجمة معاني سورة الصافات باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation .

As-Saffat


Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).

Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.

Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.

Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.

Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.

Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.

Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.

Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.

Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.

Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.

Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.

Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.

Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.

Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.

Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."

"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?

"Ashe kõ da ubanninmu na farko?"

Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."

Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.

Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."

Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.

Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.

Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.

Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.

Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?

Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.

Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.

Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."

Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.

"Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."

"Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."

"Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."

To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.

Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.

Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.

Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?

Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.

Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.

Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

Waɗannan sunã da abinci sananne.

'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.

A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.

A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.

Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.

Farã mai dãɗi ga mashãyan.

A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,

Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.

Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.

Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.

Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."

Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"

"Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"

(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"

Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.

Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."

"Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."

"Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."

"Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"

Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.

Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.

Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?

Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.

Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.

Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.

To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.

Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.

Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.

Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.

Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.

Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.

Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.

Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.

Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.

Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.

Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.

Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.

Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.

Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.

Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.

Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.

A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.

A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"

"Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"

"To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"

Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.

Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."

Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.

Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?

"Me ya sãme ku, bã ku magana?"

Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.

Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.

Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,

"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"

Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."

Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.

Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."

"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."

Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.

To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."

To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.

Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"

"Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.

Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.

Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.

Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.

Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.

Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.

Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).

Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.

Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.

Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.

Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.

Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.

Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.

Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.

Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai.

Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"

"Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"

"Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"

Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).

Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.

Aminci ya tabbata ga Ilyãs.

Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.

Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.

Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).

Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.

Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.

Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?

Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.

Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.

Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.

To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,

Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.

Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.

Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.

Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).

Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.

Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"

Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?

To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.

"Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.

Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?

Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?

Shin, bã ku tunãni?

Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?

To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.

Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"

Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.

Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,

Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.

Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.

"Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne."

"Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."

"Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."

Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,

"Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."

"Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."

Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.

Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.

Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.

Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.

Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.

Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.

Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?

To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.

Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.

Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.

Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.

Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.

Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.