ترجمة سورة الذاريات

Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
ترجمة معاني سورة الذاريات باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation .

Az-Zariyat


Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.

Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).

Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.

Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).

Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.

Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne

Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo).

Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani).

Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).

An la'ani mãsu ƙiri-faɗi.

Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.

Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"

Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.

(A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."

Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.

Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).

Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.

Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.

Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.

Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.

Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?

Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.

To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,

Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?

A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!"

Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,

Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?"

Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.

Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!"

Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi."

(Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"

Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.

"Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).

"Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."

Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.

Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.

Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.

Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.

Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"

Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.

Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.

Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.

Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"

Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.

Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.

Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.

Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.

Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,

Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.

Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.

Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.

Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."

shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.

Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.

Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.

Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.

Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.

Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.

To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.

Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
Icon