ترجمة سورة القمر

Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
ترجمة معاني سورة القمر باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation .

Al-Kamar


Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.

Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"

Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.

Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.

Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.

Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.

¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.

Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"

Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.

Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."

Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.

Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.

Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.

Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.

Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni

To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?

Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?

Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.

Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.

To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?

Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.

Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.

"Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"

Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?

Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.

Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.

Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,

To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?

Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.

Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.

Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.

Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.

Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa."

Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.

To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.

Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.

Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?

Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"

Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.

Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.

Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.

Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."

Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.

Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.

Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?

Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.

Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.

Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.

A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
Icon