ترجمة سورة القلم

Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
ترجمة معاني سورة القلم باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation .

Al-Kalam


Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.

Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.

Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.

Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.

Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.

Ga wanenku haukã take.

Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.

Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.

Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.

Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.

Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.

Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.

Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri).

Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.

Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."

Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.

Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.

Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.

Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.

Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.

Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.

Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.

Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).

"Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"

Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.

Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"

"Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."

Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"

Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."

Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.

Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."

"Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."

Haka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.

Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.

Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?

Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?

Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?

Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?

Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?

Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?

Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.

Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba.

Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).

Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.

Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.

Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?

Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?

Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.

Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.

Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.

Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"

Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.
Icon